Kano — An ga tarin jami’an tsaro a Fadar Gwamnatin Jihar Kano a ranar Litinin, sakamakon rahotannin da ke yawo kan shirin Gwamna Abba Kabir Yusuf na sauya sheƙa.
An lura da haɗaɗɗun jami’an tsaro daga Rundunar ’Yan Sanda ta Najeriya da Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) a babbar kofar shiga Fadar Gwamnatin.
Duk da cewa ba a tabbatar da shirin sauya sheƙar a hukumance ba, ana kyautata zaton gwamnan na duba yiwuwar komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Wakilinmu ya lura cewa aƙalla motoci masu sulke guda bakwai (Armoured Personnel Carriers – APCs) na ’yan sanda da DSS an ajiye su a muhimman wurare, ciki har da babbar ƙofa da kuma zagayen titi da ke kai wa Fadar Gwamnatin.
Haka kuma, an ƙara tsaurara matakan binciken tsaro, inda jami’an tsaro ke tabbatar da tantance shaidar masu shiga Fadar Gwamnatin kafin a basu izinin shiga.
