Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta bayyana cewa abokan amfani da wutar lantarki miliyan 5.36 a faɗin ƙasar nan har yanzu ba su da mita, lamarin da ke jefa su cikin haɗarin karɓar kuɗin wuta ta hanyar ƙiyasin kuɗi (estimated billing) daga kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos).
A cewar rahoton masana’antar wutar lantarki na zangon kwata na uku na shekarar 2025 da NERC ta fitar, “zuwa ranar 30 ga Satumba, 2025, abokan wutar lantarki miliyan 6.662 ne kawai daga cikin jimillar miliyan 12.030 da aka yi wa rajista kuma ke aiki a ƙarƙashin DisCos 12 aka saka wa mita, wanda ke nufin kashi 55.37 cikin 100 ne kacal ke da mita.”
Rahoton ya nuna cewa ana ci gaba da ƙoƙarin ƙara girke-girken mita, inda aka saka wa abokan amfani 228,614 mita a dukkan kamfanonin rarraba wutar lantarki a zangon kwata na uku na shekarar 2025.
“Ibadan, Aba da Abuja DisCos ne suka fi yawan girke-girken mita, inda suka wakilci kashi 23.38 cikin 100, kashi 20.81 cikin 100 da kashi 19.06 cikin 100 na jimillar mitocin da aka girka, bi da bi,” in ji rahoton.
NERC ta jaddada buƙatar ci gaba da zuba jari tare da bin tsare-tsaren girke-girken mita da aka amince da su yadda ya kamata, domin shawo kan matsalar rashin mita ga abokan wutar lantarki a ƙasar.
