Kotun Kwadago ta Ƙasa da ke Abuja ta hana likitocin “resident” a faɗin ƙasar nan shiga yajin aiki, inda ta bayar da umarnin hana yajin aikin na wucin gadi a kan Ƙungiyar Likitocin Resident ta Najeriya (NARD).
Mai shari’a E.D. Subilim ya bayar da umarnin cewa wannan hukunci na wucin gadi zai ci gaba da aiki har zuwa lokacin sauraron ƙarar a ranar 21 ga Janairu. Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (AGF) tare da Gwamnatin Tarayya ne suka shigar da ƙarar a kan NARD.
A baya dai NARD ta sanar da shirin shiga yajin aiki a duk faɗin ƙasar, bisa zargin cewa gwamnati ta gaza cika muhimman yarjejeniyoyin jin daɗi da horo da aka cimma. Shugaban NARD, Dokta Mohammad Suleiman, ya ce janye ayyukan likitocin tun daga tsakar dare na ranar Litinin martani ne ga rashin cika alkawura, sauya matsayar gwamnati da kuma tabarbarewar yanayin aiki.
“Janye ayyukan daga tsakar dare na Litinin martani ne ga alkawuran da ba a cika ba, sauya matsayar gwamnati da kuma ƙara tsananta yanayin aiki ga likitocin resident,” in ji Dokta Suleiman.
Likitochin sun bayyana manyan matsalolinsu da suka haɗa da rashin dawo da likitoci biyar da aka sallama, rashin biyan bashin ƙarin girma da albashi, da kuma rashin cikakken aiwatar da jadawalin alawus na ƙwararru (Professional Allowance Table).
“Duk matsalolin suna nan a inda suke lokacin da muka sanya hannu kan yarjejeniyar fahimta (MoU), ko ma mun koma baya,” in ji Dokta Suleiman.
Gwamnati dai ta ce an warware wasu daga cikin matsalolin, amma Dokta Suleiman ya bayyana wannan ikirari a matsayin “ruɗani”. Ya ƙalubalanci gwamnati da ta nuna inda aka ware Naira biliyan 90 da aka ce an tanada a kasafin kuɗin shekarar 2026 domin alawus-alawus na ƙwararrun ma’aikatan lafiya.
Bukatun NARD sun haɗa da dawo da likitocin biyar da aka sallama, biyan bashin ƙarin girma da aka jinkirta, da kuma amincewa da takardun shaidar ƙwarewa na likitocin ƙwararru. Ƙungiyar ta ce a shirye take ta ci gaba da tattaunawa, amma ta jaddada cewa yajin aikin zai ci gaba matuƙar ba a ɗauki matakai na zahiri ba.
A nasa jawabin, Shugaban reshen NARD na Asibitin UDUTH, Dokta Mujitaba Umar, ya ce halin da ake ciki “mai wuya ne amma babu makawa”.
Shi ma Babban Sakatare, Dokta Muhammad Abdulrahman Hassan, ya yi kira ga gwamnati da ta gaggauta ɗaukar mataki “domin amfanin al’ummar Najeriya da kuma tsarin kiwon lafiya na ƙasa baki ɗaya.”
