Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya dakatar da ɗaya daga cikin mataimakansa bayan kalamai da rahotannin kafafen yaɗa labarai da suka danganta shi da shirye-shiryen tsayawa takarar gwamnan Jihar Neja a zaɓen 2027.
Dakatarwar ta biyo bayan wata sanarwa da aka jingina wa mataimakin, wadda ake zargin ta nuna cewa ana shirin tsayar da ministan ko kuma ana la’akari da shi a matsayin ɗan takarar gwamnan Jihar Neja. Wannan kalami ya haifar da ce-ce-ku-ce da hasashe a fagen siyasa.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata, ministan ya nisanta kansa daga kalaman, yana mai bayyana su a matsayin marasa izini, da wuri, kuma ra’ayoyin kansu ne da ba su wakilci matsayinsa ko na gwamnatin tarayya ba.
Ministan Yaɗa Labarai ya jaddada cewa yana ci gaba da jajircewa wajen gudanar da aikinsa a matsayin mamba a majalisar ministocin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da tabbatar da cewa ba shi da wata aniyar tsayawa takarar gwamna a halin yanzu.
“Wannan mataimaki ya aikata hakan ne ba tare da izini ba kuma ya wuce iyakar sadarwar hukuma,” in ji sanarwar, inda ta ƙara da cewa dakatarwar ta zama dole domin tabbatar da ladabi da hana amfani da ofishin ministan wajen yada hasashen siyasa.
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da shirye-shiryen siyasa gabanin babban zaɓen 2027, inda ake danganta manyan ‘yan siyasa a sassa daban-daban na ƙasa da shirye-shiryen tsayawa takara a nan gaba.
An ce za a ci gaba da binciken cikin gida kan mataimakin da aka dakatar, yayin da ministan ya bukaci al’umma da su yi watsi da duk wani rahoton hasashe da ake yi kan makomarsa ta siyasa.









