Tsohon Antoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), yana tsare a hannun Hukumar EFCC inda ake bincikensa kan zargin kuɗin ta’addanci, wanke kuɗi, da kuma yadda aka gudanar da wasu kuɗaɗen gwamnati da aka dawo da su.
Malami, wanda ya isa ofishin EFCC a farkon makon nan, ya ci gaba da zama a tsare har zuwa misalin ƙarfe 10 na daren Talata, bayan kasa cika sharuddan belin da hukumar ta gindaya. Majiyoyi a cikin hukumar sun ce “yawan zarge-zargen” da ake masa na iya sanya a ci gaba da tsare shi na tsawon kwanaki.
Bisa ga bayanan masu bincike na EFCC, ana tambayar tsohon AGF ɗin ne kan batutuwa da dama, ciki har da: asusun banki da ake zargin na da alaka da kuɗin ta’addanci, inda suka tafi da dala miliyan 322 da aka dawo da ita daga Switzerland, lamarin dala miliyan 22 da aka samo daga tsibirin Jersey, da zargin zuba jari na Naira biliyan 10 a Jihar Kebbi, wanda ake zargin an samo kuɗaɗen ba bisa ka’ida ba. Haka kuma akwai biyan Naira biliyan 4 na shirin Anchor Borrowers da ake zargin ɗaya daga cikin matansa na iya bayar da bayani a kai.
Wani babban jami’in EFCC ya ce binciken yana da faɗi sosai kuma yana taɓa fannoni da dama na kuɗaɗen gwamnati.
“Mun tsare tsohon ministan kan batun kuɗin ta’addanci da kuma inda suka tafi da kuɗin Abacha da aka dawo da su daga Switzerland da Jersey,” in ji majiyar.
“Zuba jarinsa na N10bn a Kebbi yana ƙarƙashin bincike. Zai yiwu mu kwace wasu daga cikin kadarorin. Haka kuma wata matarsa za a iya tambayarta kan rawar da ta taka a N4bn da aka fitar daga CBN. Yana da abubuwa da yawa da zai yi bayani a kai.”
Sai dai a martaninsa, Malami ya yi watsi da zarge-zargen, yana bayyana su a matsayin “ƙarya, siyasa, da kuma rashin tushe” waɗanda suka saba da tarihin aikinsa na gwamnati.
A wata sanarwa mai tsawo da ya wallafa a X (tsohon Twitter), ya ce ba a taɓa tuhume shi, gayyata ko bincikensa kan kuɗin ta’addanci daga kowace hukumar tsaro, ta cikin gida ko ta ƙasashen waje.
“Ina bayyana a sarari cewa ban taɓa zama wanda aka tuhume ko bincika a ko’ina ba kan kuɗin ta’addanci,” in ji shi.
Malami ya ce tsohon hafsan sojan da wasu jaridu suka nakalto “ba shi ya ambace shi kai tsaye ba,” sai dai kawai ya yi magana ne kan wasu mutane da ke da hulɗar kasuwanci a kaikaice.
Yace wasu abokan siyasar sa ne ke ƙoƙarin canja yadda jama’a ke kallon lamari don “ɗaura masa alaka da ta’addanci ba tare da shaidar da ta cancanta ba.”
Ya jaddada cewa kuɗin ta’addanci babban laifi ne mai mummunan tasiri, kuma duk wani jingina mutum da shi dole ya zama bisa sahihiyar shaida.
Malami ya kuma tunatar da cewa ya jagoranci muhimman gyare-gyare da suka sa Nigeria ta fita daga jerin ƙasashen FATF masu haɗarin wanke kuɗi, yana mai cewa tarihin aikinsa “ba ya goyon bayan kowace alamar laifi.”

