Trends

ADC Ga Gwamnati: Ku Yaƙi ’Yan Bindiga Kamar Yadda Ku Ka Gaggawar Kai Doki Benin

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta yaba wa gwamnatin tarayya bisa “gaggawar da ta nuna wajen shawo kan yunƙurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin,” tana mai kira ga gwamnati da ta nuna irin wannan ƙarfin hali da jajircewa wajen yaƙar ta’addanci da ’yan bindiga a cikin gida.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na kasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta ce duk da cewa gwamnati ta nuna saurin daukar mataki a Benin, hakan “ya sake bayyana a fili yadda martanin gwamnati kan matsalolin ’yan bindiga da laifukan tarzoma a sassan Najeriya ke kasancewa mai rauni da gaj