Gilashi Mai Duhu: Rundunar ‘Yan Sanda ta FCT ta Dakatar da Aiwarta da Dokar

Benjamin Hundeyin sabon mai magana da yayun yan sanda photo credit Tribune

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta dakatar da aiwatar da dokar da ta hana amfani da gilashin mota mai duƙuwa (tinted glass) bayan wani umarnin kotu da ya dakatar da wannan aiki.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta Babban Birnin Tarayya (FCT), SP Josephine Adeh, ce ta tabbatar da hakan a cikin wata hira kai tsaye da aka yi da ita a tashar AIT a ranar Laraba.

Adeh ta bayyana cewa wannan mataki ya fara aiki ne bayan ofishin rundunar ya karɓi umarnin kotu da ya dakatar da aiwatar da wannan doka.

“Bayanan da na samu daga ofishin PRO sun tabbatar da cewa an karɓi umarnin kotu, kuma aiwatar da doka kan izinin gilashin mota mai duƙuwa yanzu an dakatar da shi har sai an yanke hukunci daga kotu,” in ji ta.

Ta ce wannan dakatarwa za ta ci gaba da aiki har sai an kammala dukkanin matakan shari’a.

“Muna jiran hukuncin kotu. Ba mu saba da kotu ba, kuma za mu ci gaba da bin tsarin doka har sai an yanke hukunci,” ta kara da cewa.

A yayin da take mayar da martani kan damuwar jama’a, Adeh ta bayyana cewa dokar gilashin mota mai duƙuwa an kirkiro ta ne don dalilan tsaro, ba don samun kuɗi ba.

Ta bayyana cewa a baya, masu aikata laifuka sun yi amfani da motocin da ke da duƙa a gilashi wajen aikata laifuka, wanda hakan ke wahalar da jami’an tsaro gano wadanda ake zargi.

“Ba mu ne muka kirkiro doka ba; mu dai masu aiwatarwa ne. Wannan doka ta samo asali ne daga bukatar tsaro,” in ji ta.

Adeh ta kuma karyata jita-jitar da ke cewa rundunar ‘yan sanda na amfani da wannan doka wajen tara kuɗi, tana mai cewa duk kudaden da ake biya don izinin gilashin mota ana tura su ne kai tsaye zuwa asusun gwamnati na TSA.

Ta tabbatar wa direbobi da jama’a cewa rundunar ‘yan sanda za ta bi umarnin kotu gaba ɗaya har sai an samu hukuncin karshe daga kotu.