Rundunar ƴan sandan Najeriya ta bayyana cewa har yanzu ba a kai mata hukuncin kotu da ya dakatar da aiwatar da dokar neman lasisin amfani da gilashin mota mai duhu (tinted glass permit) ba.
An tuna cewa wata babbar kotun tarayya da ke zaune a Warri ta umarci rundunar ƴan sanda a ranar Juma’a da ta dakatar da aiwatar da wannan doka tare da ci gaba da bin tsarin da ake kai.
Kotun ta kuma bukaci rundunar ƴan sanda da ta girmama shari’ar da ke gudana a halin yanzu.
Lauyan kare hakkin ɗan adam, Inibehe Effiong, ne ya wallafa wannan rahoto a shafinsa na X (tsohon Twitter), wanda hakan ya ja hankalin mai magana da yawun rundunar ƴan sanda na ƙasa, Benjamin Hundeyin.
Da yake mayar da martani ga wallafar, Hundeyin ya bayyana cewa har yanzu rundunar ba ta karɓi takardar hukuncin kotun da Effiong yake magana a kai ba.
Sai dai ya jaddada cewa sashen takardar hukuncin mai lamba 8, wanda ya ce “roƙo na farko, na biyu, da na uku an ƙi amincewa da su,” ba a bayyana shi cikin rahotannin da ake yadawa ba.
A cewarsa: “Ko da yake ba a kawo mana takardar hukuncin kotun da kake magana a kai ba tukuna, bari in nuna maka sashen lamba 8 (na wannan hukunci) tunda ka bar wannan bangare ka mai da hankali kawai kan lamba 6. ‘Yan Najeriya suna da hakkin sanin cikakken bayani, ba wani bangare guda kawai ba.”







