Trends

FIFA Ta Hukunta Afirka ta Kudu Saboda Saka Ɗan Wasa Mara Cancanta

Hukumar kungiyar kwallon kafa ta Duniya photo credit Alamy

Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, FIFA, ta hukunta Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka ta Kudu (SAFA) bayan da ta saka ɗan wasan tsakiyar fili, Teboho Mokoena, a wasa duk da cewa yana ɗauke da dakatarwa.

Lamarin ya faru ne a wasan neman cancantar shiga gasar cin Kofin Duniya ta 2026 da aka buga tsakanin Afirka ta Kudu da Lesotho a ranar 21 ga Maris, 2025.

A cikin hukuncin da Kwamitin Ladabtarwa na FIFA ya yanke, an bai wa Lesotho nasara da ci 3–0, an kuma ci tarar SAFA kuɗi 10,000 Swiss Francs, tare da bayar da gargadi na musamman ga Mokoena.

Wannan hukunci ya sauya lamarin a teburin rukuni C, inda Afirka ta Kudu ta rasa muhimman maki, yayin da Benin ta hau saman teburin saboda banbancin yawan ƙwallo.

Wasannin da suka rage a Rukuni C

Afirka ta Kudu: za ta buga da Zimbabwe, Rwanda

Benin: za ta kara da Rwanda, Najeriya

Rukuni C yanzu ya kasance a bude, inda za a tabbatar da ƙungiyar da za ta samu matsayi na farko kuma ta tsallake zuwa matakin gaba a ranar karshe ta wasanni.