Trends

Karancin Mai na Gabatowa Yayin da PENGASSAN ta Ayyana Yajin Aiki

Ƙungiyar Ma’aikatan Manyan Ma’aikata a Fannin Mai da Gas na Najeriya (PENGASSAN) ta umarci mambobinta a faɗin ƙasar nan da su dakatar da aiki sakamakon korar sama da ma’aikatan Najeriya 800 da kamfanin Dangote Refinery ya yi.

A cikin wata takarda da aka fitar bayan taron gaggawa na majalisar zartarwa ta ƙasa (NEC) ranar Asabar, 27 ga Satumba, 2025, wadda Sakatare-Janar Lumumba Okugbawa ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta zargi kamfanin da karya dokokin ƙwadago na Najeriya, kundin tsarin mulki da kuma yarjejeniyoyin Ƙungiyar Ƙwadago ta Duniya (ILO) ta hanyar korar ma’aikata saboda shiga ƙungiyar.

NEC ta ce kamfanin ya maye gurbin waɗanda aka kori da “mutane sama da 2,000 daga ƙasar Indiya,” lamarin da ta kira “cin zarafin dukan ma’aikata a Najeriya.”

Domin tilasta bukatunta, PENGASSAN ta umarci mambobinta a wuraren aiki su dakatar da aiki daga safiyar Lahadi, tare da ayyana rufewar aiki gaba ɗaya a ofisoshi, kamfanoni, cibiyoyi da hukumomi daga Litinin.

Takardar ta ce:
“Dukkan mambobin PENGASSAN da ke aiki a wuraren aiki su dakatar da hidimominsu daga ƙarfe 06:00 na safiyar Lahadi, 28 ga Satumba, 2025 tare da fara addu’a na sa’o’i 24. Wannan ya haɗa da duk ayyukan control room, panel operations da ma’aikatan wajen aiki.

“Dukkan mambobin PENGASSAN a ofisoshi, kamfanoni, cibiyoyi da hukumomi su dakatar da aiki daga ƙarfe 00:01 na Litinin, 29 ga Satumba, 2025.

“Babu wani tsoma baki da za a amince da shi a wuraren aiki sai inda lafiyar ma’aikata ko dukiyar kamfani take cikin haɗari; dole a nemi sahalewar babban sakatariyar ƙasa.

“Dukkan hanyoyin da suka shafi isar da gas da danyen mai zuwa Dangote Refinery su kasance an katse daga nan take.

“Dukkan rassan IOC su rage samarwa da isar da gas zuwa Dangote Refinery da petrochemicals.”

Sai dai kamfanin ya musanta korar ma’aikata da yawa.

A cewar hukumar gudanarwar kamfanin, abin da ake yi shi ne sake fasalin cikin gida don inganta aiki, tare da tabbatar da cewa mafi yawan ma’aikatan kamfanin har yanzu ‘yan Najeriya ne.

Idan aka aiwatar da wannan mataki na PENGASSAN gaba ɗaya, akwai yiwuwar ya kawo cikas ga isar da albarkatun mai zuwa Dangote Refinery, lamarin da zai iya shafar harkokin downstream da suka dogara da masana’antar.