Matatar Man Fetur da Sinadaran Dangote ta sanar da cewa ta dawo da tsarin sayar da fetur (PMS) a Naira bayan ɗan dakatarwar da aka yi kwanan nan.
Wannan ci gaban ya fito ne a cikin wata sanarwa da aka aikawa ‘yan kasuwa,
inda aka ce:
“Bayan shiga tsakani na Shugaban Kwamitin Fasaha na Naira-for-Crude, muna farin cikin sanar da ku cewa sayar da PMS a Naira ta ci gaba nan take.
“Kuna iya ci gaba da yin odarku a Naira, ko dai ku zo ku ɗauka da kanku, ko kuma mu kawo muku kyauta zuwa wuraren da aka riga aka ware a fadin ƙasa.
“Muna yaba muku bisa goyon baya da kuma ci gaba da kasuwanci da mu.”
Wannan sabon umarni ya zo ne ‘yan kwanaki bayan matatar ta dakatar da sayar da PMS a Naira. A sanarwar da aka fitar a ranar Juma’ar da ta gabata, kamfanin ya bayyana cewa yana sayar da fetur fiye da adadin da aka ware masa a tsarin naira-crude allocation, abin da ya sa ya zama ba zai iya ci gaba da sayarwa a Naira ba.
A wancan sanarwar an ce:
“Daga ranar Lahadi, 28 ga Satumba, 2025, sayar da PMS a Naira za ta tsaya. Za mu ci gaba da sanar da cikakken bayani game da dawo da sayarwa da zarar an warware matsalar.
“Abokan ciniki da suke da yarjejeniyar PMS a Naira kuma suke son mayar da kuɗinsu, an shawarce su da su gabatar da buƙata ta hukuma domin a fara aiwatar da mayar da kuɗin.”
