Trends

Gwamnatin Bayan Fage: Kotu ta Ayyana Majalisar Pat Utomi a Matsayin Haram

Mai Shari’a James Omotosho na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ya bayar da umarnin hana Farfesa na Tattalin Arzikin Siyasa, Pat Utomi, da abokan aikinsa ci gaba da shirin kafa majalisar gwamnatin bayan fage a kasar nan.

Mai Shari’a Omotosho ya bayar da wannan umarni ne a cikin hukunci kan karar da Hukumar Tsaro ta Kasa (DSS) ta shigar.

A hukuncin nasa, ya bayyana ra’ayin kafa gwamnati ko majalisar inuwa a matsayin abin da ya saba wa kundin tsarin mulkin kasa, tare da cewa wannan tsarin ba shi da tushe a tsarin mulkin shugabanci na Najeriya.

Alkali ya ce Utomi da abokan aikinsa ba za su iya fakewa da ‘yancin yin taro ko suka ga gwamnati a matsayin hujjar gudanar da ayyukan da aka ayyana a matsayin ba bisa doka ba.

Ya kuma yaba da matakin wanda ya shigar da karar, inda ya ce ya na cikin hurumin DSS ta dauki matakai da suka dace domin dakatar da duk wani abu da zai iya barazana ga tsaron cikin gida na kasa.