Tsohon Shugaban Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa jam’iyyar ba ta da wani adawa da shirin dawowar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, cikin APC.
Sai dai Ganduje, wanda shima tsohon gwamnan Kano ne, ya jaddada cewa dole Kwankwaso ya amince da wasu sharudda kafin a sake karɓarsa a jam’iyyar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wasu majiyoyi masu tushe sun tabbatar da cewa Kwankwaso ya fara tattaunawa da Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, kan batun komawarsa jam’iyyar.
A wata hira da yayi da BBC Hausa a ranar Juma’a, Ganduje ya bayyana cewa APC na tafiya ne bisa ƙa’ida da kundin tsarin mulki, don haka kowane mai son shiga dole ne ya bi waɗannan matakai.
Ya ce: “Mun ji labarin shirin dawowar Kwankwaso. A cikin dimokuraɗiyya, kuri’ar barawo da ta malami iri ɗaya ce. Don haka ba za mu rufe ƙofofi ba ga kowa.
“Duk wanda yake son shiga, an bude masa ƙofa, amma sai ya bi tsarinmu. Muna da ƙa’idoji da kundin tsarin mulki. Idan sun dawo, za mu karɓe su, amma mu fadi gaskiya: sun tofa sun kuma lashe.”
Da yake karin bayani kan taron shugabannin APC da aka gudanar a Abuja a ranar Alhamis, Ganduje ya ce taron ya gudana ne domin tantance dalilan da suka sa jam’iyyar ta fadi a zaben 2023, tare da godewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa ayyukan ci gaba da kuma nade-naden da ya yi wa mutanen Kano.
Ya kuma karyata jita-jitar da ke cewa akwai sabani tsakaninsa da Shugaba Tinubu wanda wasu ke ganin shi ne dalilin da ya sa ya ajiye kujerar shugabancin jam’iyyar.
Ganduje ya ce dangantakarsu da Tinubu ta ƙara ƙarfi fiye da da.
Ya ce: “Siyasa tana da matakai. APC tana raba mukamai bisa tsarin kowane yanki. Wani lokaci wani yanki na iya ganin mukami ya kamata ya kasance nasu. Amma tunda ba mu ke cikin siyasa don mukami ba, idan an bai wa wani yanki, sai mu ja gefe. Wannan ba matsala ba ce.
“Taron da muka yi domin gode wa Shugaba Tinubu ne. Don haka batun sabani tsakanina da shi ba ya tasowa. Abin da ke tsakanina da shi shi ne ƙauna. Zai tallafa mana, mu kuma mu tallafa masa domin mu dawo da Kano a 2027.”
Ganduje ya kuma tabbatar da cewa rikicin cikin gida a APC Kano yanzu an sasanta shi, yana mai cewa matsalar ba ta kai matsayin da ake ta yadawa ba.
