Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin tabbatar da cewa muradun ‘yan Yoruba za su kasance cikin gaba a ajandar gwamnatinsa idan ya samu nasarar zama shugaban kasa a shekarar 2027.
Wannan tabbaci ya fito ne daga wata sanarwa da mai taimaka masa wajen hulɗa da manema labarai, Kola Johnson, ya fitar ranar Alhamis, 25 ga Satumba, 2025. A cikin sanarwar, Atiku ya mayar da martani kan damuwar wasu da ke ganin wai zai fifita wasu kabilu, inda ya musanta hakan, tare da cewa ba zai taba nuna wariya tsakanin kabilu ba.
“Yoruba iyalaina ne kuma surukai na ne,” in ji Atiku, yana mai bayyana dangantakarsa ta aure da yankin tun daga shekarun 1970. Ya bayyana cewa matarsa ta farko, Titi, ‘yar Ijesha ce daga kabilar Yoruba, wacce ya aura a shekarun 70s, kuma suna da ‘ya’ya hudu tare.
“Don tunatar da wadanda ba su sani ba, matata ta farko, Titi, ‘yar Yoruba ce wacce na aura a shekarun 70s. Mun haifi ‘ya’ya hudu tare. Yanzu tana da sama da shekara 75, kuma muna tare har yanzu cikin farin ciki,” in ji shi. “’Ya’yana da muka haifa tare suna kirana ‘Baba Rere’—ma’ana uba nagari. Ina son su matuka, kuma ina ƙoƙari na kasance irin uban da kowanne namiji ya kamata ya zama.”
Atiku ya bayyana Titi a matsayin “Jewel of Inestimable Value” wato “Gimbiya mai daraja,” yana jaddada irin rawar da mutanen Yoruba suka taka a rayuwarsa da harkokinsa na siyasa. Ya kara da cewa, mafi yawan abokansa na kusa da shi tun tsawon shekaru ‘yan Yoruba ne.
“Ina da halin mu’amala da kowa ba tare da kallon kabila ko addini ba. Tun kafin na shiga siyasa, na saba da kowa daga bangarori daban-daban na kasar nan,” in ji shi.
Ya kuma tabbatar da cewa yankin Kudu maso Yamma zai kasance cikin manyan abubuwan da zai ba fifiko a mulkinsa idan Allah ya ba shi nasarar zama shugaban kasa.
“Saboda haka, muradun ‘yan Yoruba za su kasance a gaba a cikin fifikon gwamnatina, idan na samu damar zama shugaban kasa a 2027 da yardar Allah,” in ji shi.
Atiku, wanda ya zo na biyu a zaben shugaban kasa na baya inda ya sha kaye a hannun Shugaba Bola Tinubu, ana sa ran zai sake fafatawa da Tinubu a zaben 2027.
