Dan wasan gaba na Faransa da Paris Saint-Germain, Ousmane Dembélé, ya zama zakaran kyautar Ballon d’Or 2025, wanda ya tabbatar da matsayinsa a cikin manyan fitattun ’yan kwallon duniya.
An sanar da nasarar tasa a dandalin Théâtre du Châtelet dake Paris, inda aka taru cikin murna da mamaki.
Ga da dama, wannan nasara ta fi zama lashe kyauta ɗaya kawai – ita ce alamar farfadowa da nasara bayan jinya da rashin daidaito da suka hana shi haske a Barcelona. Motsa zuwa PSG ya bude masa sabon mataki na buga wasa, inda ya kammala kakar da ta fi kowace nasara a rayuwarsa.
Dembélé, mai shekaru 28, ya doke matashin tauraron Barcelona da Spain, Lamine Yamal, ya kuma gaji dan wasan tsakiya na Manchester City, Rodri, wanda ya lashe kyautar a 2024.
Hasken kakar 2024–25
A kakar 2024–25, Dembélé ya buga kwallo mafi kyau tun farkon aikinsa. Ya fara kakar a gefen dama na harin PSG, amma kocin Luis Enrique ya mayar da shi mai kai farmaki (striker), matakin da ya zama dabarar nasara.
A Ligue 1, ya zura kwallaye 21 tare da taimakawa sau 8 a wasanni 29, ya raba kyautar babbar mai cin kwallo kuma ya shiga cikin Team of the Year. Amma shine bajintarsa a Champions League da ya karfafa damar lashe Ballon d’Or.
Ya zura kwallaye 8 a gasar, ciki har da kwallaye kan manyan kungiyoyi kamar Manchester City, Liverpool da Arsenal. Haka kuma ya bayar da taimako 6, ciki har da wanda ya bada nasara a wasan kusa da karshe da Arsenal da kuma biyu a wasan karshe da Inter Milan.
“Lashe Ballon d’Or ga dan kwallo shi ne mafi girma na kashin kai,” in ji Dembélé ga France Football a watan Yuni.
“Abu ne da kake mafarki tun kana karami… ganin kwallon nan, Ballon d’Or, abu ne na musamman.”
Ya kuma zura kwallaye biyu a wasanni 7 da ya buga wa Faransa a 2024–25. Wannan ya sanya shi zama na shida daga Faransa da ya taba lashe kyautar, kuma na biyu a karni na 21 bayan Karim Benzema a 2022.
Lamine Yamal, mai shekaru 18, ya kare na biyu tare da lashe Kopa Trophy a karo na biyu, yayin da Vitinha na PSG (Portugal) ya kare na uku, sannan Mohamed Salah na Liverpool ya kare na hudu.
Cole Palmer na Chelsea da Ingila ya shiga cikin na takwas.
Zakaran bara, Rodri na Spain, bai shiga jerin masu takara ba saboda jinya.
Gyokeres ya lashe kyautar Gerd Muller
Dan wasan gaba na Arsenal, Viktor Gyokeres, ya lashe Gerd Muller Trophy na babbar mai cin kwallo a Turai (kulob da kasa) a 2024–25.
Ya zura kwallaye 54 a wasanni 52 da Sporting (Portugal), da kuma 9 a wasanni 6 da Sweden a Nations League. Ya koma Arsenal a kan kudi har £64m.
Kyautar ta fara a 2021, kuma wadanda suka taba lashe ta sun hada da Robert Lewandowski (sau biyu), Erling Haaland, Harry Kane da Kylian Mbappé.
Lamine Yamal ya sake lashe Kopa Trophy
Ko da yake bai lashe Ballon d’Or ba, Lamine Yamal ya sake lashe Kopa Trophy – kyautar matashi kasa da shekara 21 – karo na biyu a jere.
Ya taimaka wa Barcelona lashe La Liga da Copa del Rey, inda ya zura kwallaye 18 da taimako 21 a wasanni 55.
Ya kuma kai Spain zuwa wasan karshe na Nations League, inda suka sha kashi a hannun Portugal, bayan ya zura kwallaye biyu a nasarar 5-4 a kan Faransa ta Dembélé a wasan kusa da karshe.
Luis Enrique ya zama kocin shekara
Kocin PSG, Luis Enrique, ya lashe kyautar kocin shekara 2024–25 bayan jagorantar PSG lashe Champions League na farko a tarihin kulob din, tare da kammala treble duk da rasa Mbappé a farkon kakar.
Haka kuma kyautar Socrates Award (ta ayyukan jin kai) ta tafi ga Xana Fundacion, asusun da iyalin Enrique suka kafa don tallafa wa yara masu cututtuka masu barazana ga rayuwa, a tunawa da ’yarsa Xana wacce ta rasu a 2019 tana da shekaru 9.
Donnarumma ya lashe Yashin Trophy karo na biyu
Gianluigi Donnarumma, tsohon mai tsaron ragar PSG wanda yanzu yake Manchester City, ya lashe kyautar Yashin Trophy na mafi kyawun mai tsaron gida.
A kakar da ta gabata, mai shekaru 26 din ya kare gida a wasanni 17 daga cikin 47 kafin ya koma City kan £26m.
Ya taba lashe kyautar a 2021 bayan Euro 2020.
Alisson Becker na Liverpool ya kare na biyu, yayin da Emiliano Martinez na Argentina (Aston Villa) wanda ya lashe ta sau biyu a baya, ya kare na takwas wannan karon.
