Fadar shugaban kasa ta mayar da martani ga tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, wanda ya yi ikirarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shirin mayar da kansa shugaban ƙasa har abada.
A karshen mako da ya gabata, lokacin da El-Rufai ya gana da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ya ce alamu na nuna Tinubu na kokarin zama kamar shugaban Kamaru, Paul Biya, wanda ke rike da mulki tun daga shekarar 1982.
El-Rufai ya ce dukkanin shaida da Tinubu ya yi na kare dimokuraɗiyya “bogi” ne, domin gwamnatin yanzu ta fara karkata zuwa mulkin kama karya.
Sai dai a martanin da ya fito daga Mai Ba wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Bayani da Dabaru, Mista Bayo Onanuga, ya ce, “Shugaba Tinubu dan dimokuraɗiyya ne, kuma ba ya da niyyar ci gaba da zama a ofis bayan 28 ga Mayu, 2031, lokacin da aka sake zabarsa a 2027.”
Onanuga, wanda ya nuna cewa shugaban jam’iyyar ADC na iya bukatar taimako, ya ce El-Rufai ya riga ya gane cewa shirin abokansa a sabuwar jam’iyyarsa na hana Tinubu sake lashe zabe a 2027 ya zama abun banza, kuma “misalin tafiya wadda ba za ta kai ko ina ba.”
Ya kuma ce El-Rufai ya yi mamakin irin tarbar da Shugaba Tinubu ya samu a Kaduna kwanan nan, abin da ya sabawa ikirarin da yake yi cewa yankin Arewa ya juya baya ga shugaban kasa.
A cikin wani sakon da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Onanuga ya rubuta cewa:
“Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana a matsayin wanda ke bukatar taimako, musamman ganin irin kalaman sa marasa tushe da zargi da yake yadawa kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
“Ya bayyana a sarari cewa El-Rufai ya fahimci cewa shirin abokansa a sabuwar jam’iyyarsa na hana Shugaba Tinubu lashe zaben 2027 ya zama ba zai yiwu ba. Wannan shiri ya riga ya mutu tun kafin ya fara.
“Bayan rahotannin tarbar ban girma da Shugaba Tinubu ya samu a Kaduna ranar Juma’a, El-Rufai ya karye saboda irin goyon bayan da shugaban kasa ke ci gaba da samu daga Arewa. Wannan ya saba wa labarin da yake yadawa cewa yankin ya ki Tinubu.
“A sakamakon haka, sai ya koma kan labaran ƙarya, ciki har da cewa Shugaba Tinubu na son zama shugaban kasa har abada bayan 2027 – wani zargi da babu tushe kuma abin dariya.
“Shugaba Tinubu dan dimokuraɗiyya ne wanda ba shi da niyyar ci gaba da zama a ofis bayan 28 ga Mayu, 2031, bayan sake lashe zaben 2027.
“Gwamna Uba Sani na iya tuntubar wanda ya gada, domin El-Rufai na iya amfana daga shawarar kwararru don fid da shi daga wadannan tunani na hauka da labaran ƙarya da yake kirkira kan Tinubu da 2027,” in ji shi.
