A yayin shirye-shiryen babban zabe na 2027, fiye da mambobi 200 na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a mazabar Gubuchi, karamar hukumar Makarfi ta jihar Kaduna sun fice daga jam’iyyar.
Rahotanni sun nuna cewa an karɓi masu sauya shekan ne zuwa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a ranar Litinin.
Tun bayan da hadakar shugabannin hamayya suka amince da amfani da ADC a matsayin dandamalin takararsu a zaben mai zuwa, ana ta samun sauya sheka daga jam’iyyun da suka hada da PDP, LP da ma APC kanta zuwa jam’iyyar.
Shugabannin hamayya – tsohon gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai – wadanda ke cikin wannan hadaka, suna ci gaba da karɓar sabbin mambobi a ADC.
A karshen mako, akalla mambobi 10,000 daga PDP, APC da sauran jam’iyyun siyasa sun sauya sheka zuwa ADC a karamar hukumar Agatu ta Jihar Benue.
