Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa Najeriya ta dade tana fuskantar rashin samun shugabanni nagari, inda ya ce shugabannin da ake da su tsawon shekaru sun kasance marasa inganci.
Sarkin ya kuma yi gargadi cewa da ba a cire tallafin man fetur ba, da ƙasar ta riga ta karye.
Ya yi wannan bayani ne a lokacin bikin Kano International Poetry Festival (KAPFEST) karo na biyu, wanda aka gudanar a Kano ranar Asabar, karkashin shirye-shiryen Poetic Wednesdays Initiative (PWI).
A cewar Sarkin, kyakkyawan shugabanci ne kadai zai iya ceto ƙasar daga halin da take ciki yanzu.
Ya ce, “Ingancin shugabanci shi ne ginshiƙin nasarar kowace al’umma, kuma Najeriya ta daɗe tana da shugabanni marasa inganci. Ba za ka iya ba da abin da ba ka da shi ba, har sai mun fara kula da irin mutanen da muke zaɓa don shugabantar mu. A mafi yawan lokuta a wannan ƙasa, idan ka kalli shugabannin da ke jagorantar ka, sai ka ce ‘Ya Allah, shin wannan shi ne mutum? Ta yaya muka kai ga wannan hali?’”
Sanusi ya nuna damuwa kan yadda tattaunawa a Najeriya ke ci gaba da karkata kan bambancin ƙabila da addini, maimakon muhawara kan ci gaban zamani da fasahar da duniya ke magana akai.
Ya ƙara da cewa, “Kalli sauran ƙasashe suna tattauna batutuwan canjin yanayi, suna magana kan artificial intelligence. Amma mu a nan har yanzu muna tattauna batutuwan da muka gada tun shekarun 1960 – Hausa, Igbo, Yarbawa, Arewa ko Kudu, Musulmi ko Kirista. Wannan shi ne babban koma baya.”
Sarkin ya kalubalanci matasa da su tashi tsaye su karɓi ragamar mulkin ƙasa daga tsofaffin shugabanni, inda ya ce da ƙuduri matasa za su iya yin ritayar da su gaba ɗaya.
Game da cire tallafin mai, Sanusi ya ce: “Tallafin man fetur ba shi da ɗorewa. Da har yanzu muna ci gaba da shi, da Najeriya ta riga ta karye. Idan kuɗaɗen da aka kashe a tallafi an zuba su a matatun mai, da yanzu muna cin gajiyar su. Abin da nake adawa da shi shi ne tallafin da ake bayarwa kan amfani, wanda ke ƙara buɗe masana’antu a Turai da ba da ayyuka ga su, amma ba mu da. Idan a 2012 aka ɗauki matakin da ya dace, da yanzu ba mu kasance a wannan hali ba.”
Ya kuma yi gargadi cewa yadda gwamnatoci a ƙasar ke ci gaba da aro kuɗi suna ɓata su, zai yi mummunan tasiri a tattalin arzikin ƙasa nan gaba.
A nasa jawabin, Daraktan Shirye-shiryen PWI, Nasiba Babale, ta bayyana cewa taron KAPFEST na bana, wanda taken shi ne “Poetry in a Time of Crisis,” ya nufin tunatar da mawaƙa da masu fasaha yadda za su yi amfani da waƙoƙin su wajen wayar da kan jama’a da kuma yaɗa zaman lafiya a lokacin rikice-rikicen da Arewa ke fama da su.
