Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bai wa wani kwamiti na Majalisar Zartarwa ta Kasa (FEC) umarnin gaggawa domin ɗaukar matakai da za su taimaka wajen rage farashin abinci a fadin Najeriya.
Ministan Jiha na Ma’aikatar Noma da Tsaron Abinci, Aliyu Sabi Abdullahi, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin wani taron horaswa na musamman ga manema labarai na majalisar dattawa a Abuja.
Ya ce umarnin shugaban kasa ya fi karkata ne kan tabbatar da cewa kayan amfanin gona suna samun hanya cikin aminci a dukkanin hanyoyin sufuri, domin rage tsadar jigilar kayayyaki.
“Shugaban kasa ya bayar da umarni kai tsaye, tare da wani kwamiti na Majalisar Zartarwa da ke kula da yadda za a tabbatar da aminci wajen safarar kayayyakin gona a hanyoyinmu daban-daban a kasar nan,” in ji Abdullahi.
Ministan ya ƙara da cewa wannan mataki ya yi daidai da hangen nesa na Tinubu kan samun ‘yancin kai a fannin abinci, wanda ba kawai ya tsaya kan wadatar abinci ba, har ma ya shafi rage tsada, samun sauƙin siya da kuma ingancin abinci ta hanyar dorewa.
Haka kuma, gwamnatin tarayya tana shirin ƙaddamar da shirin kula da lafiyar ƙasa ta manoma domin ƙara yawan amfanin gona, tare da wani sabon tsarin sauya tsarin ƙungiyoyin haɗin gwiwa (cooperatives) domin tara albarkatu da kuma ƙarfafa manoma a ƙauyuka.
“Shugaban kasa ya nuna matuƙar sha’awa kan harkar ƙungiyoyin haɗin gwiwa a matsayin wata hanya ta tattara albarkatu, samar da ayyukan tattalin arziki da kuma inganta rayuwar mambobi,” in ji Abdullahi.
