Majalisar Dattawa ta Ki Amincewar Natasha ta Koma Aiki Bayan Wata Shida

Sanata Natasha mai wakiltan Kogi ta Tsakiya

Majalisar Dattawan Najeriya ta ki amincewa da bukatar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta koma bakin aiki a majalisa.

A wata wasika da Mukaddashin Magatakardan Majalisar Dokoki ta Kasa, Dr. Yahaya Danzaria, ya sanya wa hannu, majalisar ta tabbatar da cewa ta samu sanarwar daga sanatar cewa za ta koma aiki daga 4 ga Satumba, 2025, bayan cikar wa’adin dakatarwarta.

Sai dai majalisar ta bayyana cewa dakatarwar nata wadda ta fara daga 6 ga Maris, 2025 na nan daram har sai Kotun Daukaka Kara ta yanke hukunci a kan karar da ta shigar tana kalubalantar wannan hukunci.

“Matsalar tana gaban kotu (sub judice), kuma har sai an kammala shari’ar, ba za a iya daukar matakin gudanarwa da zai bai wa ke damar komawa aiki ba,” in ji wasikar.

A ranar Lahadi, lauyan Akpoti-Uduaghan, Victor Giwa, ya shaida wa manema labarai cewa sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya za ta koma bakin aiki tare da abokan aikinta daga 23 ga Satumba.

“Gaskiya, ta shirya komawa bakin aiki. Tana birnin Landan a yanzu. Komai ya kammala, kuma wa’adin watanni shida ya cika. Abin da kawai ya rage shi ne komawarta,” in ji Giwa.

Ya kara da cewa shugabancin majalisar dattawa ma ya nuna shirye-shiryen tarbar ta ba tare da wata matsala ba.

Sanata Akpoti-Uduaghan an dakatar da ita a watan Maris bayan majalisar ta zargeta da karya dokokin cikin gida na majalisar. Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tabbatar da dakatarwar, lamarin da ya sa ta daukaka kara zuwa Kotun Daukaka Kara.

Dr. Danzaria ya jaddada cewa majalisar dattawa za ta sake duba dakatarwar ne kawai bayan kotu ta yanke hukunci.