Kungiyar Ƙwadago ta Najeriya (TUC) ta yi Allah wadai da shirin Gwamnatin Tarayya na saka kudin haraji 5% a kan kayayyakin man fetur, tana kiran matakin a matsayin “wulakancin tattalin arziki da rashin tausayi.”
A cewar gwamnati, kudin zai zama hanyar da za a sami kuɗin gina tituna tare da rage gibin da ake da shi a fannin manyan ayyukan raya ƙasa. Shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan manufofin kudi da gyaran haraji, Taiwo Oyedele, ya ce sama da ƙasashe 150 suna da irin wannan mataki, wasu ma da kaso mafi girma.
Sai dai a martanin su, shugaban TUC, Festus Osifo, da sakataren janar, Nuhu Toro, sun fitar da sanarwa tare da buƙatar gwamnati ta janye shirin cikin kwanaki 14. Sun yi gargadin cewa idan ba a yi hakan ba, za su kaddamar da yajin aikin kasa baki ɗaya, domin tuni dukkan ƙungiyoyin da ke ƙarƙashin su an sanya su cikin shirin gaggawa.
Kungiyar ta bayyana cewa ‘yan Najeriya tuni sun durƙushe da tarin haraji, cire tallafin man fetur, hauhawar farashin mai da kayan abinci, da kuma raunin Naira. Ƙara wani sabon haraji, in ji TUC, zai ƙara jefa mutane cikin tsananin wahala, ya lalata sana’o’i, kuma ya ƙara tura jama’a cikin talauci.
“Wannan shiri tsantsar mugun tattalin arziki ne,” in ji kungiyar. “Gwamnati ba za ta ci gaba da yin amfani da ‘yan ƙasa a matsayin ragon gwaji ba. Maimakon kawo sauƙi da dama, kullum sai ƙirƙiro sabbin hanyoyin tsotse jama’a. Mun gaji!”
TUC ta jaddada cewa yajin aiki yana nan a matsayin babbar dama idan gwamnati ta yi kunnen uwar shegu da gargadin. Haka kuma ta bukaci kungiyoyin farar hula, kwararru, dalibai, shugabannin addini da kasuwanni su haɗa kai wajen ƙin wannan manufofin danniya, tana mai cewa ‘yan Najeriya sun fi cancantar adalcin tattalin arziki fiye da hukunci marar iyaka.


