Rundunar ‘Yan Sanda ta Ƙasa Ta Naɗa Hundeyin Sabon Mai Magana da Yawunta

Benjamin Hundeyin sabon mai magana da yayun yan sanda photo credit Tribune

Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Adeolu Egbetokun, ya amince da naɗin Chief Superintendent of Police (CSP) Benjamin Hundeyin a matsayin sabon Mai Magana da Yawun Rundunar ‘Yan Sanda ta Ƙasa (FPRO).

Hundeyin, gogaggen ɗan sanda kuma ƙwararren mai sadarwa, ya gaji DCP Olumuyiwa Adejobi, wanda ya sanar da mika ragamar ofishin a ranar Alhamis, 4 ga Satumba, 2025, a Abuja.

Sabon FPRO ɗin ya samu digiri na farko BA (Hons) a harshen Turanci daga Jami’ar Jihar Legas, da kuma digiri na biyu MSc a Legal Criminology and Security Psychology daga Jami’ar Ibadan. Haka kuma ya karɓi takardar shaidar Civil-Military Coordination daga Martin Luther Agwai International Leadership and Peacekeeping Training Centre, Jaji, Kaduna.

Hundeyin ƙwararren masani ne a fannin hulɗa da jama’a. Yana da alaƙa da ƙungiyoyi da dama, ciki har da kasancewarsa Associate na Nigerian Institute of Public Relations (NIPR), Memba na International Public Relations Association (IPRA), da kuma Associate na Chartered Institute of Personnel Management of Nigeria (CIPM).

Ayyukansa sun taɓa kai shi muƙamai daban-daban masu muhimmanci, ciki har da kasancewa Mai Magana da Yawun ‘Yan Sanda na Zone 2 Command, Onikan, Legas, da kuma Administration Officer a Sashen Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sanda, Abuja.

A shekarar 2020, Hundeyin ya kasance cikin tawagar Najeriya a United Nations Peacekeeping Mission a Darfur, Sudan. Kafin wannan naɗi, shi ne Mai Magana da Yawun Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Legas.

Sufeto-Janar Egbetokun ya yi kira gare shi da ya yi amfani da ƙwarewarsa a fannin sadarwa da tsaro domin ƙarfafa amincewar jama’a da kuma kyautata alaƙar rundunar da ‘yan Najeriya.