Matan Rivers: ‘Karɓar Kuɗin Ba Tare da Zuwa Ba Zamba Ce’ – Yan Sanda

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Rivers ta yi gargaɗi ga mata kan wata sabuwar dabi’a da ke ƙara yawaita ta karɓar kuɗin haya daga maza domin zuwa saduwa ko alƙawari, amma daga baya ba sa bayyana. Rundunar ta ce wannan ɗabi’ar laifi ce mai nasaba da zamba ta hanyar yaudara wacce doka za ta hukunta.

A cikin wata sanarwa, rundunar ta bayyana cewa an samu koke-koke da dama daga mutanen da suka ce sun aika wa wasu mata kuɗin haya, amma daga bisani matan sun kashe wayoyinsu ko suka ƙi bayyana a wurin da aka yi alƙawari.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar ya jaddada cewa irin wannan ɗabi’a ta na ɗauke da laifi ƙarƙashin doka, inda ya bukaci jama’a su rika kai rahoto ga hukumomi idan an ci zarafinsu a irin wannan hanya.

Rundunar ta kuma yi gargaɗi cewa ba za ta lamunci duk wata makarƙashiya ta zamba a ƙarƙashin sunan alaƙar soyayya ba, tare da yin kira ga mata da su guji irin wannan aiki, sannan ta shawarci maza da su yi hattara.