Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai bar Abuja a yau domin fara hutu na shekara ta 2025 tare da yin aiki a lokacin hutu a ƙasashen Turai.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar, inda ya bayyana cewa hutun zai ɗauki kwanaki goma na aiki.
A cewar sanarwar, Shugaba Tinubu zai shafe waɗannan kwanaki tsakanin ƙasashen Faransa da Birtaniya, sannan daga nan ya dawo gida Najeriya.
