’Yan sanda a jihar Ekiti sun kama wani mutum mai suna Ibrahim bisa zargin kashe saurayin ’yarsa.
An gurfanar da Ibrahim a gaban kotun majistare ta jihar Ekiti a ranar Laraba, 3 ga Satumba, 2025, inda aka tura shi gidan gyaran hali.
Ana zargin Ibrahim da bugun saurayin har lahira bayan ya gano dangantakarsa da ’yarsa. Lamarin ya faru ne lokacin da mamacin ya ziyarci budurwarsa a gidan mahaifinta, kusa da Corpers’ Lodge da ke kan titin New Iyin, Ado-Ekiti.
Rahotanni sun bayyana cewa mahaifin, wanda bai amince da soyayyar ba, ya tara ’yan uwansa inda suka yi wa saurayin dukan kawo wuka, wanda daga bisani ya rasu sakamakon yawan jinin da ya zube daga raunukan da ya samu.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar Ekiti, Sunday Abutu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, “An gurfanar da mahaifin yarinyar tare da wasu mutane biyu kuma an tura su gidan yari.”
