Gwamnonin Arewa maso Gabas na Najeriya sun bayyana cewa matsalar tsaro a yankin ba za ta warware da aikin soja kaɗai ba, sai an haɗa hanyoyin daban-daban na magance ta.
Yayin taron na 12 na Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas da aka gudanar a jihar Taraba ranar Asabar, Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce ilimi, kiwon lafiya, tsaro, da ingantattun hanyoyin sufuri su ne ginshikan dawo da zaman lafiya da ci gaban yankin.
Zulum ya yabawa kokarin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wajen yaki da ta’addanci, amma ya nuna damuwa cewa talauci, rashin aikin yi, da rashin ingantattun hanyoyin mota na ci gaba da haifar da rikice-rikice a yankin.
“Dole mu sake nanata bukatar mu na mafita ta hanyar hanyoyin da ba na soja kadai ba. Wannan ya haɗa da magance tushen matsalar ta hanyar samar da ayyukan yi ga matasa ta hanyar bunkasa ilimin fasaha da sana’o’i, inganta hanyoyin sufuri, farfaɗo da harkar noma, inganta shirye-shiryen rage talauci, tsaro, da kiwon lafiya,” in ji Zulum.
“Dole mu ɗauki matakan da za su tabbatar da farfaɗo da yankinmu. Dole mu yi aiki tukuru wajen jawo hannun jari daga cikin gida da kuma ƙasashen waje, da kuma ƙarfafa kafa masana’antun manya da ƙanana.”
A cikin taron, Gwamnonin sun roƙi gwamnatin tarayya da ta tallafawa masu zuba jari na cikin gida da na waje domin bunkasa kananan da matsakaitan sana’o’i a yankin.
Tun da farko, Gwamnan Taraba, Dr. Agbu Kefas, ya bukaci abokan aikinsa su matsa wa Hukumar Cigaban Arewa maso Gabas (NEDC) lamba domin gyara gadar Namai da ta rushe a watan Agustan 2024, wacce ta yi sanadin rasa rayuka.
Gwamnonin sun jaddada cewa yankin na fama da manyan kalubalen jin ƙai da gina muhalli, amma sun tabbatar da aniyarsu na ci gaba da tura shirye-shiryen cigaba.

