Kakakin jam’iyya: ADC Ta Nesanta Kanta da Bolaji Abdullahi

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bayyana cewa tsohon Ministan Wasanni, Bolaji Abdullahi, ba shi da wani matsayi na kakakin jam’iyyar ko sakataren yaɗa labarai, kamar yadda ya ke ikirari.

A wata sanarwa da Dr. Christopher O. Okechukwu, Daraktan Harkokin Watsa Labarai na ofishin shugaban jam’iyyar na ƙasa, ya fitar a ranar Alhamis, ADC ta ce ikirarin Abdullahi na cewa shi ne kakakin jam’iyyar ya saba da ƙa’idojin jam’iyyar, kuma ya zama barazana ga tsarin shugabanci.

“Jam’iyyar ADC ta ga dacewar ta yi bayani kan wani batu mai muhimmanci da ya shafi wakilcin jam’iyyarmu. Mun lura cewa Malam Bolaji Abdullahi yana ta gabatar da kansa a matsayin Kakakin ADC. Wannan ba gaskiya ba ne, kuma ya saba da tsarin da ake bi wajen irin waɗannan mukamai,” in ji Okechukwu.

Jam’iyyar ta bayyana sharuddan da ake buƙata kafin mutum ya iya zama kakaki ko sakataren yaɗa labarai:

  1. Sai mutum ya kasance cikakken mamba mai rijista a jam’iyyar ADC.
  2. Sai ya cike fom ɗin neman mukami tare da samun sa hannu daga akalla mutane uku daga kowace jiha 36 da kuma FCT.
  3. Sai kuma ya fito da nasara a zaɓe na taron gangamin ƙasa.

Okechukwu ya ce Bolaji Abdullahi bai cika ko ɗaya daga cikin waɗannan sharudda ba, don haka ba shi da ikon yin magana da sunan jam’iyyar.

“Ci gaba da ikirarin da yake yi yana ƙasƙantar da martabar ADC. Muna kira gare shi da ya dakatar da amfani da sunan jam’iyya da mukaman da ba shi da izini a kai,” in ji shi.

Jam’iyyar ta kuma ja hankalin kafafen yaɗa labarai da su tabbatar da tushe kafin wallafa bayanai, tare da gargadin cewa yin dogaro da Abdullahi a matsayin kakakin jam’iyyar zai iya yaɗa ƙarya da kuma bata martabar ADC.

“Muna kira ga ‘yan jarida da gidajen labarai da su yi taka-tsan-tsan wajen bayar da rahoto. Yin amfani da bayanan mutane da ba su da hurumin magana da sunan ADC zai yaudari jama’a tare da rage amincin da al’umma ke da shi ga kafafen yaɗa labarai,” in ji Okechukwu.

ADC ta sake jaddada kudurinta na yin mulki bisa dimokuraɗiyya, gaskiya da riƙon amana, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da kare sahihancin bayananta ga jama’a.