Trends

2027: Zan Nemi Takarar Shugabancin Ƙasa a Jam’iyyar ADC — Amaechi

Rotimi Amaechi Tsohon gwamnan Jihar Rivers photo credit Punch

Tsohon Gwamnan Jihar Rivers kuma tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya sake jaddada aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin ƙasa a zaɓen 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).

Amaechi ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin tattaunawa da ‘yan jarida a jihar Kano, bayan ganawarsa da gamayyar ‘yan kasuwa.

Tsohon Ministan ya jaddada cewa ba zai ja da baya ko ya sauka wa wani ɗan takara ba a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.

“Zan tsaya takarar fidda gwanin shugabancin ƙasa a ADC, kuma da ikon Allah ina fatan nasara don in fuskanci Tinubu a 2027. Ba zan sauka wa kowa ba, jama’a ne za su tantance wanda suke so ya jagorance su,” in ji shi.

Amaechi ya yi kira ga jam’iyyar ADC da ta tabbatar da sahihin tsarin zaɓen cikin gida, yana mai cewa hakan zai ƙarfafa dimokuraɗiyya a cikin jam’iyyar.

Ya kuma soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, inda ya ce ‘yan Najeriya sun gaji da manufofinta saboda tsananin ƙuncin rayuwa da ake fuskanta a ƙasar.

“Ko gwamnati na so ta gudanar da sahihin zaɓe ko ba ta so, abu ɗaya ya tabbata — lokaci ya ƙure. ‘Yan Najeriya sun gaji, babu wanda yake farin ciki a ƙarƙashin Tinubu, ko a Rivers, ko a Kudu baki ɗaya. Wahala ta mamaye kowa,” in ji Amaechi.

Dangane da nadin mukaman siyasa, Amaechi ya zargi gwamnatin da rashin nuna adalci da haɗa kai na gaskiya, inda ya ce ‘yan tsiraru da ke kusa da shugaban ƙasa ne kawai aka sakawa, alhalin an bar sauran yankuna cikin rashin jin daɗi.

Da aka tambaye shi game da batun tsarin rabon mulki (zoning) a ADC, Amaechi ya ce wannan hukunci ya rataya ne a hannun shugabancin jam’iyya, amma ya jaddada cewa zai ci gaba da kasancewa cikin takara duk da kowanne irin mataki da jam’iyyar ta ɗauka.

Ya bayyana kansa a matsayin ɗaya daga cikin mafi cancantar masu neman shugabanci a Najeriya.

“Idan ka dubi dukkan ‘yan takara, ciki har da Tinubu, wa ya fi ni shiri? Takarata za ta kawo haɗin kai domin ni daga Kudu nake, kuma ba mu da wata matsala da kowace jiha ko yanki,” in ji shi.

A kan ikirarin cewa tasirinsa a Jihar Rivers ya ragu saboda tasirin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, Amaechi ya yi watsi da wannan magana.

“A kwanakin baya, lokacin da na ziyarci Rivers don kaddamar da ADC, taron jama’a ya yi matuƙar girma daga filin jirgin sama har zuwa wajen taron, kuma babu wanda ya biya kuɗin ɗaukar su. Wannan ya isa ya nuna maka inda mutane suke tsaye,” in ji Amaechi.