Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) ta dakatar da dukkanin zirga-zirgar jirgin kasa a hanyar Abuja–Kaduna bayan hatsarin da ya faru a ranar Lahadi, inda jirgi ya yi hatsari.
Manajan Darakta na NRC, Kayode Opeifa, ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da aka yi a Abuja. Ya bayyana cewa ba za a ci gaba da zirga-zirgar ba sai an kammala bincike tare da tabbatar da cikakken tsaro.
Opeifa ya ce tawagogin kwararru daga NRC, Hukumar Binciken Tsaro ta Najeriya (NSIB) da sauran hukumomi masu alaka sun isa wajen hatsarin domin gano musabbabin lamarin da kuma bayar da shawarwari kan hanyoyin kauce wa irin haka nan gaba.
Ya karyata rade-radin da ke cewa rashin kula da gyaran jiragen ne ya haddasa hatsarin, yana mai jaddada cewa hukumar tana bin tsauraran ka’idojin tsaro a dukkan ayyukanta. A cewarsa, an mayar wa fasinjojin da abin ya shafa kudaden su.
Shugaban NRC ya kara da cewa fasinjoji shida ne suka samu raunuka kadan a hatsarin, kuma tuni suka samu kulawar likitoci. Ya ce adadin fasinjojin da ke cikin jirgin a lokacin lamarin har yanzu ana tantancewa.
A halin da ake ciki, hukumar NSIB ta kaddamar da bincike na musamman kan hatsarin, yayin da hukumomi ke kara kaimi wajen dawo da zirga-zirgar jirgin a hanya cikin tsaro da inganci.

