’Yan sandan jihar Neja sun kama wata budurwa mai shekaru 23 mai suna Sarah Ogbonna bisa zargin satar wayoyin salula da kuɗi da darajarsu ta kai Naira miliyan 29 daga shagon da take aiki a matsayin yar kasuwa a Obasanjo Commercial Complex, Minna.
Rahotanni sun nuna cewa wacce ake zargi, mazauniyar Okada Road, Minna, ta yi amfani da wani ɓangare na kuɗin wajen kama haya da gyara wani gida da ta bai wa saurayinta Samuel Bello (wanda yanzu ya tsere) a unguwar Sauka-Kauta, Minna. Haka kuma ta aika masa da wasu kuɗaɗe ta hanyar canja wurin banki.
Kakakin rundunar ’yan sanda na jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya bayyana cewa Sarah ta amsa laifin a yayin bincike, inda ta ce tana shiga wata rukunin ƙungiyar yanar gizo da ke tara kuɗi na mako-mako, inda take bada N150,000.
Haka kuma, ’yar uwarta babba Mercy Ogbonna mai shekaru 30, ta shiga hannu, bayan gano cewa Sarah ta rika aikawa da ita kuɗaɗe domin magance matsalolin gida, ciki har da biyan haya da sayen kayan abinci.
Binciken ya kuma kai ga cafke wasu mutane biyu: Ruth Emmanuel (23), wadda itama yar kasuwa ce a shagon, amma ta daina aikin bayan ta shiga cikin harkar satar, da kuma Nurudeen Musa (32) na Obasanjo Complex, wanda ake zargin ya sayi wayoyin da aka sace sannan ya rika sayarwa da farashi mai sauƙi.
DSP Abiodun ya ce an cafke Sarah ranar 8 ga watan Agusta bayan mai shagon, wanda dillalin waya ne a Obasanjo Complex, ya kai rahoto.
“Da zarar rahoton ya iso, jami’anmu suka cafke Sarah, ta kuma amsa cewa tana aikata hakan tun daga shekarar 2023, amma ba ta san adadin da ya kai Naira miliyan 29 ba. Sai dai an gano kuɗi N700,000 a wajenta nan take. Bayan wannan bayani ne aka kama sauran mutanen da ake zargi ranar 9 ga watan Agusta, 2025,” in ji kakakin rundunar.
Ya ƙara da cewa bincike ya tabbatar da cewa Sarah ta aika da kuɗaɗe da dama ga babbar ’yar uwarta Mercy domin taimaka mata wajen biyan bukatun gida, ciki har da haya da kayan masarufi.
Source Premium Times



