Trends

Shettima ya Ziyarci Gwamna Ododo Domin Ta’aziyya Rashin Mahaifinsa

Kashim Shettima a filin jirgin jihar kogi. Photo credit The Guardian

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya isa jihar Kogi a yau Laraba domin yin ta’aziyya ga Gwamna Usman Ahmed Ododo kan rasuwar mahaifinsa, marigayi Alhaji Ahmed Momohsani Ododo.

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa tare da tawagarsa sun iso filin saukar jirgin sama na Obajaba Airstrip da safiyar Laraba, inda aka tarbe su da girmamawa.

Rahotanni sun bayyana cewa jerin motocin Mataimakin Shugaban Ƙasa, wanda Mataimakin Gwamnan Jihar Kogi, Joel Salifu Oyibo, ke jagoranta, ya bar filin saukar jirgin kai tsaye zuwa Upogolo, Okene, gidansu na iyali domin jajanta wa Gwamna Ododo da danginsa.