Trends

Binciken Dala Miliyan 7.2: EFCC Ta Rufe Asusun Bankin Mele Kyari

Kolo Mele Tsohon Shugaban Matatar Mai na NNPCL

Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) ta saka tsohon Babban Darakta Janar na Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), Mele Kyari, a jerin mutanen da ake sa ido a kansu, sakamakon binciken da ake yi kan dala biliyan $7.2 da aka ware domin gyaran matatun mai, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne bayan da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin dakatar da wasu asusun banki guda huɗu da ake danganta da Kyari, bisa zargin almundahana.

Majiyoyi daga EFCC sun shaida wa wakilinmu a ranar Talata cewa binciken ayyukan NNPCL a lokacin da Kyari yake jagoranta ya kai wani mataki mai zurfi a watan da ya gabata bayan cafke wasu daga cikin abokan hulɗarsa.

An ruwaito cewa an sha tambayar waɗannan abokan hulɗar kan yadda aka yi amfani da kuɗaɗen da aka ware domin gyaran matatun mai na ƙasar.

Majiyoyi sun kuma tabbatar cewa jami’an bincike sun samu takardu da muhimman bayanai kan yadda aka yi mu’amala da kuɗin gyaran matatun mai.

Wani babban jami’in EFCC, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba za a gayyaci Kyari domin amsa tambayoyi.

“Ina tabbatar muku mun yi nisa da binciken shi (Kyari). Kada a manta a binciken laifuka, iyakokin ƙasashe ba su da tasiri. Ko mutum ya bar ƙasa ko bai bar ba, ba zai hana bincike ba, domin duk lokacin da muka buƙace shi, za mu same shi, kuma tuni yana cikin jerin waɗanda muke sa ido a kansu,” in ji jami’in.

Wani majiyar EFCC ya ce: “Muna binciken shi (Mele Kyari) kuma binciken ya yi nisa. Ta yaya za a ce ba za mu bincike shi ba, alhali tuni muna binciken waɗanda suke kusa da shi?

“Dalilin da ya sa hukumar ba ta fito da sunansa ba shi ne mu samu bayanai masu muhimmanci. Muna yin taka-tsantsan ne saboda akwai jami’ai da dama da abin ya shafa.”

Ƙoƙarin samun karin bayani daga mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya ci tura, domin bai ɗauki kiran waya ba, haka kuma bai amsa saƙon rubutu da aka aika masa ba.

A watan Afrilu, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauke Mele Kyari daga mukamin Babban Darakta Janar na NNPCL, tare da rushe shugabannin hukumar gaba ɗaya, inda aka naɗa Bashir Ojulari a matsayin sabon shugaban kamfanin daga ranar 2 ga Afrilu, 2025.

Bayan sauke Kyari, EFCC ta fara binciken manyan tsoffin jami’an NNPCL ciki har da daraktocin matatun mai uku, domin gano yadda aka yi da kuɗaɗen gyaran da har yanzu bai sa matatun suka fara aiki ba.

Alƙali Emeka Nwite a ranar Talata ya bayar da umarnin dakatar da asusun Kyari bayan sauraron buƙatar da lauyan EFCC, Ogechi Ujam, ya shigar karkashin lamba FHC/ABJ/CS/1641.

Sai dai maimakon kwanaki 60 da EFCC ta nema, Alƙali Nwite ya iyakance dakatarwar zuwa kwanaki 30, tare da sharadin cewa za a iya sabunta ta idan akwai buƙata.

Lauyan EFCC ya shaida wa kotu cewa wannan umarni ya zama wajibi domin asusun bankin na cikin bincike da ya shafi laifin hada baki, cin zarafin ofis da kuma wanke kuɗi, har zuwa kammala binciken.