Trends

2027: Amaechi Ba Shi da Cancantan Zama Shugaban Ƙasa – Wike

Nyesom Wike Minista Birnin Tarayya

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya yi watsi da burin tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, na yin takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027, inda ya bayyana shi a matsayin “wanda ya mutu tun kafin ya fara.”

Wike, wanda ya yi magana a shirin Politics Today na tashar Channels Television a ranar Talata, ya ce ’yan Najeriya ba za su ba Amaechi dama ba a babban zaɓen gaba, yana mai jaddada cewa ba zai samu tikitin takara na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ba.

“Shi (Amaechi) ma ya san ba zai samu tikitin ba. Na karanta cewa ya ce yana sanin raunin shugaban ƙasa, don haka zai iya kayar da shi. Amma a 2022 ma ya san raunin shugaban ƙasa, amma shugaban ya kayar da shi ba tare da wahala ba a cikin fidda gwani,” in ji Wike.

A cewar Wike, tarihin mulkin Amaechi ya isa ya hana ’yan Najeriya ɗaukar shi da muhimmanci.

“’Yan Najeriya sun san mutumin ƙarshe da za su ba tikiti, saboda sun san wannan yunƙurin nasa (na Amaechi) ya mutu tun kafin ya fara,” ya ƙara da cewa.

Tsohon gwamnan jihar Rivers ɗin ya kuma zargi magabacinsa da rashin mutunta doka da tsarin shari’a a lokacin da yake gwamna daga 2007 zuwa 2015.

“Ba zai iya yaƙi da cin hanci da rashawa ba, ba zai iya samar da kyakkyawan shugabanci ba, domin bai mutunta kotu da tsarin mulki ba a lokacin da yake gwamnan Jihar Rivers,” Wike ya bayyana.

Amaechi, wanda ya jagoranci jihar Rivers daga watan Mayu 2007 zuwa Mayu 2015, ya fice daga jam’iyyar APC zuwa ADC a shekarar 2025 domin cimma burin sa na shugabancin ƙasa. Tun da farko, ya tsaya takara a fidda gwanin shugaban ƙasa na APC a 2022, inda ya zo na biyu bayan tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu.

Wike da Amaechi, dukansu tsofaffin gwamnonin Jihar Rivers, sun dade suna gaba da juna a siyasa, abin da har yanzu ke tasiri a siyasar jihar mai arzikin man fetur ta Niger Delta.