Trends

Tinubu Ya Soke Harajin Kashi 5%na Sadarwa — NCC

Bola Ahmed Tinubu Shugaban Kasar Nigeriya

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya soke harajin kashi 5% da ake ɗora wa kan ayyukan sadarwa, matakin da aka bayyana zai rage wa ’yan kasa da kamfanoni nauyin kuɗi a tattalin arzikin zamani na dijital.

Shugaban Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), Aminu Maida, ne ya bayyana hakan a lokacin taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Talata.

Maida ya tabbatar da cewa wannan haraji, wanda aka dakatar tun a shekarar 2023, yanzu an cire shi gaba ɗaya karkashin sabbin dokokin haraji na ƙasa.

“Harajin kashi 5% ba ya nan yanzu,” in ji shi. “A da dai an dakatar da shi kawai, amma Shugaban Ƙasa ya soke shi baki ɗaya. Na kasance a wurin lokacin da aka tattauna batun, kuma ya ce a fili: ‘A’a, ba za mu ɗora wannan nauyi kan ’yan Najeriya ba.’ Na yi matuƙar farin ciki ganin wannan umarni ya samu tabbaci a cikin sabuwar doka.”

Harajin, wanda ya shafi kira da amfani da bayanai (data) na intanet, ya jawo ƙarin suka daga masana’antar sadarwa da ƙungiyoyin kare mabukata, inda suka yi gargadin cewa zai ƙara tsadar amfani da intanet da kuma kawo cikas ga ayyukan kamfanonin sadarwa da ke fama da tsadar gudanarwa.

Shugaba Tinubu ya fara dakatar da harajin a watan Yuli 2023 a matsayin wani ɓangare na sauye-sauyen manufofin kuɗi da aka yi domin rage nauyin haraji masu yawa da ke kan ’yan kasuwa da gidaje. Dakatarwar ta zo ne ta hanyar jerin umarnin shugaban ƙasa da ya sanya hannu a kansu bayan ya hau mulki.

Sai dai a watan Oktoba 2024, Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta kawo batun dawo da harajin a matsayin wata hanya ta ƙara samun kuɗaɗen shiga, wanda ya haɗa da haraji a kan caca, wasannin saɓo da kuma lottiri.

Wannan shawara ta gamu da tsananin adawa daga masana’antar sadarwa.

Ƙungiyar Kamfanonin Sadarwa ta Najeriya (ATCON) ta bayyana cewa dawo da harajin zai ƙara tsadar sabis, ya kuma kawo cikas ga bunƙasar masana’antar, musamman a wannan lokaci da samun ingantaccen intanet ke zama ginshiƙi ga tattalin arzikin Najeriya.