Ruwan Sama Mai Tsananin Karfi Ya Lalata Gidaje Da Dama a Yobe

Ambaliyan ruwa a jihar Yobe

uwan sama mai tsananin karfi da aka tafka a ranar Juma’a ya yi mummunar barna a Potiskum, Jihar Yobe, inda ambaliyar ruwa ta wanke ta kuma rusa gidaje da dama a sassa daban-daban na garin.

Ruwan sama wanda ya fara da dare a ranar Alhamis kuma ya ci gaba har zuwa safiyar Juma’a ya bar mutane da dama cikin kangin rashin matsuguni bayan gidajensu sun lalace ko kuma sun rushe gaba ɗaya.

Mafi yawan yankunan da suka fi shan wahala sune wadanda ke kusa da koguna, inda illar ambaliyar ta fi tsanani saboda yawancin gine-ginen sun rushe.

Wadannan yankuna sun hada da Arikime, Ramin Kasa, Tandari, Nahuta, Boriya, Rugar Fulani, da Unguwar Kuwait.

Sauran wuraren da abin ya shafa sun hada da Old Prison, Filin Nashe, Unguwar Makafi/Majema, Unguwar Jaji Bakin Kwari, Afghanistan, Tsangaya Bakin Kwari, Karofi, Bayan Garejin Danjuma, da yankunan da ke bayan Fudiyya Potiskum.

Mutanen wadannan yankuna na fuskantar matsalar ambaliyar ruwa akai-akai saboda rashin isassun magudanar ruwa. Saboda haka, ruwan sama baya samun hanyar fita, wanda ke haddasa mummunar barna.

A lokacin hada wannan rahoton, bayanai sun nuna cewa ba a tabbatar da samun mutuwa ba, amma gidaje da dama sun ruguje. A daya daga cikin wuraren da abin ya shafa, wani gini ya rushe a kan wata mata, amma ta tsira cikin ikon Allah.

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) ta tura jami’anta domin taimakawa wadanda abin ya shafa.