Rashin halartar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a wasu muhimman tarukan gwamnati ya haifar da jita-jitar cewa yana fama da rashin lafiya, sai dai Fadar Shugaban Ƙasa ta gaggauta karyata wannan zargi.
Cibiyar Bincike Mai Zaman Kanta (ICIR) ta rawaito daga wasu majiyoyi cewa tawagar likitocin shugaban ƙasa na shirye-shiryen yiwuwar tura shi ƙasashen waje domin neman gaggawar kulawar lafiya.
Bisa ga bayanan da ICIR ta tattara, an ce shugaban ƙasa ya kwanta rashin lafiya na tsawon kwanaki, abin da ya sa bai halarci wasu muhimman ayyukan gwamnati ba. A sakamakon haka, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya wakilci shugaban ƙasa a wasu tarukan hukumomi.
Haka kuma, ICIR ta ce wani ma’aikacin Fadar Aso Rock ya bayyana cewa an soke wasu daga cikin ayyukan shugaban tun farkon mako, tare da tsaftace ragowar jadawalin makonsa domin bai wa tawagar likitoci damar sa ido a kan lafiyarsa.
Sai dai mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan bayani da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya shaida wa ICIR cewa “Mutane na taɗa jita-jita marasa tushe.”
Ya jaddada cewa shugaban yana aiki. “Jiya (5 ga Agusta) yana ofishinsa. Na shiga na gaishe shi. Yana nan yana aiki,” in ji shi.
A daren jiya, jaridar Daily Trust ta sake tuntubar Onanuga wanda ya ƙaryata jita-jitar rashin lafiyar shugaban.
Dangane da dalilin da yasa shugaban bai halarci tarurruka na jama’a tun makon da ya gabata ba, Onanuga ya ce shugaban na iya zaɓar yin aiki daga gida.
“Babu abin da ke damun shugaban ƙasa, yana cikin koshin lafiya. Yana iya yin aiki daga gida, ko daga duk inda yake so. Ina tabbatar muku babu matsala da lafiyarsa,” in ji mai magana da yawun shugaban ƙasa.
Bisa ga ICIR, an gan shi a bainar jama’a na ƙarshe a ranar Juma’a, 1 ga Agusta, inda ya halarci taron buɗe taron Progressive Media Summit mai taken, “Bayyana Muhimmancin Sabbin Kafofin Sadarwa a Ci gaban Ƙasa.”
A wajen taron, shugaban ya bayyana cikin koshin lafiya tare da ƙarfafa matasa masu aiki a kafofin sada zumunta su yi amfani da kafafensu wajen cigaban ƙasa.
Kwanaki kafin wannan, a ranar 29 ga Yuli, shugaban ya jagoranci taron tarbar kungiyar Super Falcons bayan nasarar da suka samu a gasar WAFCON a Morocco. Ya tsaya tsawon lokaci yana taya ƙungiyar murna tare da sanar da kyaututtuka masu yawa ga ‘yan wasa da masu horar da su, lamarin da ya jawo muhawara a jama’a.
Sai dai rashin halartar shugaban ƙasa wajen tarbar ƙungiyar D’Tigress da ta samu nasara a ranar 3 ga Agusta ya haifar da tambayoyi, musamman ganin cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima ne ya wakilce shi a wannan bikin.

