Trends

Majalisar Dokokin Neja Ta Nemi Haramta Bukukuwan “Sign-Out” a Makarantu

Makarantar Sakadare a Nigeriya

Majalisar Dokokin Jihar Neja ta bukaci Gwamna Mohammed Umaru Bago da ya fitar da umarnin zartarwa domin haramta bukukuwan “Marker’s Day” da “Sign-Out” a dukkanin makarantun sakandare da manyan makarantu masu zaman kansu da na gwamnati a fadin jihar.

Wannan bukata ta biyo bayan kudirin da dan majalisa mai wakiltar mazabar Tafa, Hon. Muhammad Sani Idris ya gabatar, inda ya nuna damuwa kan yadda bukukuwan irin su ke kara zama hanyar nuna rashin da’a, halaye marasa kyau da kuma ayyukan da ba su dace ba daga dalibai.

A cewar Hon. Idris, “al’adar ‘signing out’ da ake yi domin murnar kammala karatu, musamman daga daliban ajin karshe, ta rikide zuwa wani abu mai hadari wanda ke dauke da halaye marasa kyau da rashin ladabi.”

Ya ce tun asali, wannan biki na “sign-out” an kirkires hi ne domin bai wa daliban da suka kammala karatu damar yin murnar cimma nasarar karatunsu, amma abin ya canza zuwa wani abin da ke haifar da matsala a kokarin gina tarbiyyar dalibai masu ladabi da rikon amana.

Dukkan sauran ‘yan majalisar sun goyi bayan kudirin, suna mai cewa koke-koken jama’a dangane da lamarin ya nuna cewa lokaci ya yi da gwamnati za ta dauki mataki na gaggawa.

Mataimakiyar Shugabar Majalisar, Hon. Afiniki Dauda, wadda ta jagoranci zaman, ta bayyana cewa za ta tuntubi Gwamnan Jihar da Ma’aikatar Ilimi ta Jiha domin tabbatar da aiwatar da haramcin cikin gaggawa.