Masu Amfani da Rijiyar Burtsatse a Lekki Na Iya Shan Ruwan Kashi – Gwamnatin Lagos

Babajide Sanwo- Olu, Gwamnan Lagos

Gwamnatin Jihar Legas ta bayyana damuwa game da ingancin ruwan da mazauna yankin Lekki ke sha, inda ta yi gargaɗi cewa wadanda ke amfani da rijiyoyin burtsatse (borehole) na iya kasancewa suna shan ruwan da ya ƙazantu da najasa.

Babban Sakatare na Ofishin Ayyukan Ruwa da Magudanan Ruwa, Injiniya Mahmood Adegbite, ne ya bayyana hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar kwanan nan a jihar.

Adegbite ya bayyana cewa rashin sarrafa ruwan najasa yadda ya kamata a yankin Lekki yana barazana ga lafiyar mazauna yankin, domin ruwan najasa na iya shiga cikin ruwan ƙasa da ake amfani da shi ta hanyar rijiyar burtsatse.

“A game da sarrafa ruwan najasa, zan iya cewa duk wanda ke tono rijiyar burtsatse a yankin Lekki yana iya kasancewa yana shan abin da zan kira ‘ruwan doya da kashi’,” inji shi.

Ya bayyana cewa gwamnati na da shirin tace duk ruwan najasa a yankin don dakile yaduwar cututtuka da za su iya biyo baya.

“In har muka samu damar tace dukkan ruwan najasa a wannan yanki, za mu iya kawar da duk wata cuta da ka iya biyo bayan rashin tacewa,” Adegbite ya ƙara da cewa.

A kan batun ambaliya kuma, Adegbite ya ce duk da ƙoƙarin da gwamnati ta yi wajen gina hanyoyin magudanar ruwa, har yanzu akwai aiki da dama da ya rage a gaba. Ya danganta ruwan sama mai yawa da aka samu a lokacin da ake sa ran samun ruwan kadan da rikice-rikicen muhalli.

“Jiya ruwa ya yi yawa matuka, wanda ba a saba da haka ba a wannan lokacin da ake kira August break. Amma hakan na faruwa ne saboda wasu dalilai masu rikitarwa. Ko da yake gwamnati ta zuba jari sosai, har yanzu muna bukatar ƙarin aiki a wannan fanni,” inji shi.

Gwamnatin jihar ta bukaci mazauna Lekki da su kasance masu lura da lafiyarsu, tare da ci gaba da bibiyar hanyoyin samun ruwan da ya dace da amfani.