Rikicin PDP Ya zo Karshe a Halin Yanzu – Wike

Nyesom Wike Minista Birnin Tarayya

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, a ranar Litinin ya bayyana cewa rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ya lafa a halin yanzu, sakamakon ficewar wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar.

Wike ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja, inda ya mayar da martani kan ficewar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar daga jam’iyyar.

Duk da haka, tsohon gwamnan jihar Rivers ya ce har yanzu akwai wasu batutuwa da jam’iyyar ke bukatar warwarewa domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

Ya bayyana wasu sharuɗɗa da ya ce dole ne a bi domin a samu zaman lafiya na dindindin a cikin jam’iyyar PDP.

Wike ya dage cewa dole ne a amince da sakamakon zaɓen shugabannin yankin Kudu maso Kudu da aka gudanar.

A cewarsa, kotu ta amince a gudanar da taron, don haka babu wanda zai iya soke sakamakon.

“Zaɓen shugabannin yankinmu na Kudu maso Kudu da aka gudanar dole ne a amince da shi. Babu tantama, babu wata hanya ta daban,” in ji shi.

“Lokacin da muke gudanar da taronmu na Kudu maso Kudu, mukaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa ya yi ikirarin cewa gwamnonin PDP ba su goyi bayan taron na ƙasa ba. Ina su gwamnonin PDP yanzu? Mun gudanar da taronmu a Calabar, kuma babu wanda zai shawo kanmu akai.”

“Ina so in jaddada cewa idan suna so su janyo wani sabon rikici, to hakan ya rage musu. Amma taron ya gudana yadda ya kamata, kuma Chief Dan Orbih ya fito a matsayin Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Kasa daga wannan taro. Kuma kotu ta amince a gudanar da taron,” in ji Wike.

Channels TV