An Sace Wata Jaririya a Asibitin Ekiti

An sace wata jaririya a cibiyar lafiya ta Okeyinmi da ke Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti.

Wani ganau ya bayyana cewa an gano bacewar jaririyar ne da safiyar ranar Litinin lokacin da nas-nas da ke aiki suka je su duba lafiyarta.

Lamarin ya haifar da fargaba da tashin hankali a cikin harabar asibitin.

Ma’aikatan da ke aiki a dakin haihuwa, mahaifiyar jaririyar, jami’in tsaro da wasu da ake zargi an tafi da su ofishin ‘yan sanda domin ci gaba da bincike.

Wasu ’yan kasuwa da ke kusa da asibitin sun bayyana alhini da mamaki kan satar jaririyar.

Da aka tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na ‘Yan Sanda, SP Sunday Abutu, ya tabbatar da cewa an kama mutane hudu da ake zargi da hannu a lamarin kuma suna ba da sahihan bayanai da za su taimaka wa bincike.

Abutu ya kara da cewa Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, Mr. Joseph Eribo, ya bayar da umarnin a mika lamarin ga sashen binciken manyan laifuka na jihar (CID) domin gudanar da cikakken bincike da kuma tabbatar da cewa an ceto jaririyar.