Kungiyar kwallon kafa ta Galatasaray ta kaddamar da sabbin ‘yan wasanta, dan wasan gaba na Najeriya Victor Osimhen da kuma dan wasan gefe na Jamus Leroy Sané, a gaban dubban magoya baya a filin wasa na RAMS Park ranar Asabar kafin wasan sada zumunta da za su fafata da Lazio daga Serie A na Italiya.
Wannan biki ya kasance daya daga cikin mafi jan hankali a tarihin kwallon kafa ta Turkiyya, inda dubban masoya suka cika filin wasa na Ali Sami Yen Sports Complex domin kallon wannan gagarumin taron da aka gudanar cikin hasken wuta, kide-kide da shagulgula domin maraba da shahararrun ‘yan wasan duniya guda biyu.
Wannan biki ya nuna kammala daya daga cikin manyan kasuwannin canja sheka da Galatasaray ta taba yi, inda suka samu sabbin ‘yan wasa manya guda biyu domin karfafa tawagar da za ta fafata a gasar Turai bayan lashe gasar Super Lig ta kasar.
Osimhen, mai shekaru 26, ya koma Galatasaray daga Napoli ta hanyar dindindin bayan wata kakar aro mai ban mamaki da ya zura kwallaye 37 tare da taimakawa aka ci guda 8 a wasanni 41, inda ya taimaka wa kungiyar ta lashe kofin Super Lig da kuma kofin Turkiyya. Cinikin na Osimhen ya kai €75 miliyan – mafi tsada a tarihin kwallon kafa ta Turkiyya.
Cikin wannan ciniki, Galatasaray za ta biya €40m a gaba daya, tare da €5m a matsayin karin kudi (bonuses), sauran kudin kuma za a raba su cikin shekaru biyu masu zuwa. Napoli kuma za ta samu kashi 10 cikin 100 daga duk wani cinikin gaba da za a yi da Osimhen. Ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru hudu inda zai rika karbar €15m a duk shekara, baya ga kudin tallace-tallace da hoton sa.
Sané kuwa ya iso a matsayin dan wasa mara kwantiragi daga Bayern Munich, inda ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru uku da darajarsa ke tsakanin £10 zuwa £11m a kowace shekara. Zuwa Sané zai kara wa Galatasaray saurin kai hari da kuma kwarewa a gasar zakarun Turai (Champions League).
Jami’an kulob din sun bayyana cewa taron kaddamarwar na iya samar da kudin shiga na kimanin €6m zuwa €7m daga tallace-tallace, kayan wasanni, da kudin shiga daga tikiti – wanda ke nuna karfin kasuwancin da wadannan sabbin ‘yan wasa suka zo da shi.
Taron kaddamarwar ya biyo bayan sanarwar da mataimakin shugaban Galatasaray, Abdullah Kavukcu, ya yi ranar Juma’a, inda ya bayyana cewa Osimhen ya sadaukar da babban kudi domin ganin ya kammala komawarsa dindindin zuwa kulob din.
“Adadin kudin da Victor ya sadaukar domin zuwa nan abin al’ajabi ne. Ya fasa karbar kudi da babu wani dan wasa da zai fasa, kuma muna matukar farin cikin samun sa,” in ji Kavukcu a lokacin taron manema labarai.
Jami’in na Galatasaray ya bayyana cewa samun Osimhen ba tare da karya tsarin kudi na kulob din ba babban nasara ne ga Galatasaray da ma kwallon kafa ta Turkiyya baki daya.
A da akwai bukatu daga kungiyoyi da dama irin su Juventus da kuma kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya. A watan Yuni, Osimhen ya ki amincewa da tayin albashin €40m a shekara daga Al-Hilal, yana mai zabar Galatasaray da albashi mai sauki na €15m a shekara.
A cikin hirarsa ta farko da gidan talabijin na kulob din a YouTube, Osimhen ya bayyana jin dadinsa da wannan mataki, yana mai cewa Galatasaray ce wuri mafi dacewa da zai nuna kwarewarsa gaba daya.
“Wannan ne wurin da zan iya bayyana kaina gaba daya ta hanyar kwallo da kuma dukkan abin da nake da shi,” in ji Osimhen. “Ina matukar godiya ga duk wanda ya taimaka wajen ganin na iso nan. Na zo ne domin ina kaunar wannan wuri kuma ina jin dadi sosai anan.”
Tuni dai magoya baya sun tarbe shi cikin murna da shagali a tashar jirgin saman Atatürk a Istanbul, inda dubban masoya suka cika tituna suna murnar isowarsa cikin farinciki da kauna.



