Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ƙaddamar da sabbin littattafan ilmantar da masu zaɓe domin magance raguwar fitowar jama’a da kuma rashin sha’awar zaɓe gabanin babban zaɓen 2027.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, INEC ta ce an samar da wannan shiri ne tare da haɗin gwiwa da ƙungiyar Kimpact Development Initiative (KDI) da sauran abokan hulɗa na cikin gida da na ƙasashen waje.
Sabbin kayan sun haɗa da sabunta Littafin Ilmantar da Masu Zaɓe na Ƙasa da kuma wani littafi na musamman da aka mayar da hankali kan matasa, wanda aka tsara domin ƙarfafa fahimtar harkokin jama’a da shiga cikin zaɓe, musamman ga matasan Najeriya.
Shugaban Kwamitin Bayanai da Ilmantar da Masu Zaɓe na INEC, Mohammed Haruna, ya bayyana cewa yawan masu fitowa zaɓe ya ragu daga sama da kashi 60 cikin ɗari a 2003 zuwa ƙasa da kashi 30 cikin ɗari a zaɓukan baya-bayan nan, yana danganta hakan da ƙarancin ƙwarin gwiwa da rashin isasshen ilimi kan zaɓe.
Da yake gabatar da muhimmin jawabi a madadin Shugaban INEC, Kwamishinan Ƙasa, Joashà Amupitan (SAN), ya yi gargadin cewa rashin sha’awar zaɓe babbar barazana ce ga dimokuraɗiyyar Najeriya, yana mai cewa dokoki kaɗai ba za su iya magance matsalar ba. Ya ce, “Jama’a marasa sha’awa alama ce ta dimokuraɗiyya da ke ja da baya.”
Jagorar KDI, Bukola Idowu, ta bayyana littattafan a matsayin wani muhimmin mataki da aka tsara bisa la’akari da sabbin dokokin zaɓe, ci gaban fasaha, da kuma sauye-sauyen halayen masu zaɓe. Ta ƙara da cewa littafin da aka tanadar wa matasa an tsara shi ne domin jawo hankalinsu a matsayin masu zaɓe, masu wayar da kai, da kuma wakilan sauyi.
Daraktar Ilmantar da Masu Zaɓe da Wayar da Kai ta INEC, Victoria Eta-Messi, ta ce yanzu littafin ya dace da Dokar Zaɓe ta 2026, inda ya ƙunshi batutuwa kamar zaɓen fidda gwani na jam’iyyu, kudaden kamfe, laifukan zaɓe, da kuma amfani da fasahohi irin su Bimodal Voter Accreditation System (BVAS).
An tsara littattafan cikin sassa guda 11, tare da haɗa ka’idojin duniya da kuma dabarun zamani na dijital domin isa ga al’ummar Najeriya masu amfani da fasaha, da nufin dawo da amincewar jama’a da kuma ƙara yawan masu fitowa zaɓe a 2027.
