Trends

Yajin Aiki: Har Yanzu Ba a Biya Bukatun mu Ba – Likitocin FCT

Likitoci yayin da suke zanga - zanga

Kungiyar Likitocin Ma’aikatan Horaswa ta Babban Birnin Tarayya (ARD-FCTA) ta bayyana cewa duk da janye yajin aikin da ta fara ba tare da iyaka ba, babu daya daga cikin bukatunta da aka biya zuwa yanzu.

A yayin kaddamar da aikin titin Northern Parkway daga Ring Road II zuwa Ring Road III a kan Shehu Yar’Adua Way, kusa da Life Camp a Abuja, Ministan FCT, Nyesom Wike, ya ce ya amince da dukkan bukatun likitocin.

“Ina yabawa likitocin da suka janye yajin aikin, gwamnati ta ji dadin wannan fahimtar da suka nuna. Na sanya hannu kan dukkan bukatunsu da aka gabatar a teburina a yau,” in ji Wike.

Sai dai shugaban kungiyar, Dr George Ebong, ya shaida wa Daily Trust cewa an dakatar da yajin aikin ne bayan shiga tsakani na kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da kananan hukumomi da al’amuran FCT.

“Kwamitin Majalisar Dattawa kan Kananan Hukumomi da Al’amuran FCT ya shiga tsakani. Duk da cewa har yanzu babu bukatunmu da aka cika, sun tabbatar mana cewa za su yi magana da Minista, kuma taronmu ya yarda mu ba su amana,” in ji shi cikin sako na WhatsApp.

Ya kara da cewa shawarar janye yajin aikin ta samo asali ne daga girmamawar da kungiyar ke yi wa kwamitin majalisar, darajar da take bai wa Ministan FCT, da kuma kulawar da take da ita ga marasa lafiya.

“Girmamawar mu ga kwamitin Majalisar Dattawa, mutuntakar mu ga Ministan FCT da kuma kaunar mu ga marasa lafiya sune dalilan da suka sa muka dakatar da yajin aikin, tare da fatan za a cika bukatunmu. Dole mu ci gaba da ceton rayuka kamar yadda muka rantse,” in ji shi.

ARD-FCTA ta shiga yajin aikin ba tare da iyaka ba a ranar Litinin, saboda abinda ta bayyana a matsayin gazawar gwamnati wajen warware bukatunta, duk da cewa ta fara yajin gargadi na mako guda a baya.

Bukatun likitocin sun hada da:

Yanayin rashin ingancin walwala,

Rashin biyan albashi a kan lokaci,

Rage albashi ba tare da bayani ba,

Karancin ma’aikata sosai,

Damuwa ta kwakwalwa sakamakon dogon lokacin aiki,

Rashin daukar sababbin ma’aikata a asibitocin FCT tun daga 2011.