Trends

Take Doka: PCN Ta Rufe Shagunan Magani 572 a Jihar Filato Saboda

Hukumar Kula da Harkokin Magunguna ta Kasa (PCN) ta rufe kantunan sayar da magunguna da shagunan Patent Medicine guda 572 a Jihar Filato bisa laifukan karya dokokin harkokin magunguna, ciki har da gudanar da ayyukan jinya ba bisa ka’ida ba, samun damar amfani da magungunan da ake sarrafawa ba tare da izini ba, har ma da yin girki a cikin shagunan magunguna.

Aikin sa ido da binciken, wanda ya gudana na tsawon kwanaki hudu a kananan hukumomi bakwai na jihar, ya tantance wurare 778 da suka hada da kantunan magunguna 199, shagunan Patent Medicine 499 da kuma wurare 80 da ke gudanar da harkokin sayar da magunguna ba bisa ka’ida ba.

Daga cikin wuraren da aka bincika, an rufe kantunan magunguna 120, shagunan Patent Medicine 372 da kuma wurare 80 na haramtattun masu sayar da magunguna.

Shugaban Sashen Tabbatar da Bin Doka na PCN, Dakta Suleiman S. Chiroma, ya ce wannan mataki na ci gaba da cire wadanda ba kwararru ba daga sarkar samar da magunguna tare da gyara matsalolin da suka shafi wuraren adana magunguna.

Ya ce, “Wannan mataki yana da matukar muhimmanci wajen kawar da yaduwar jabun magunguna da marasa inganci.”

Chiroma ya bayyana cewa kashi 60 cikin 100 na kantunan magunguna da aka ziyarta an rufe su saboda rashin bin ka’idoji. Ya kara da cewa kashi 26 cikin 100 kacal na wuraren da aka bincika kantunan magunguna ne, yayin da mafi yawansu shagunan Patent Medicine ne ko kuma masu gudanar da harkokin sayar da magunguna ba bisa ka’ida ba.

Daga cikin laifukan da aka gano akwai gudanar da ayyukan jinya ba tare da izini ba, adanawa da rarraba magunguna ba bisa ka’ida ba, samun damar shiga wuraren adana magungunan guba ba tare da izini ba, da kuma gaza gabatar da ingantattun lasisi.

Ya yi gargadin cewa irin wadannan ayyuka na jefa lafiyar jama’a cikin hadari tare da barazana ga tsaron kasa, domin magungunan da ake sarrafawa na iya fadawa hannun masu aikata laifuka da ‘yan ta’adda.

Hukumar ta kuma bayyana cewa kashi 40 cikin 100 ne kawai na kantunan magunguna da aka bincika suka cika ka’idojin aiki yadda ya kamata, lamarin da ke nuna yawaitar rashin bin dokoki a fannin. Haka kuma, an bayar da umarnin gyara kura-kurai guda biyar ga wasu wuraren da aka bincika.

A nasa bangaren, Magatakardar Hukumar, Pharm. Ibrahim Babashehu Ahmed, ya sake jaddada kudirin PCN na aiwatar da sauye-sauyen da za su taimaka wajen cimma manufar Samar da Ingantaccen Kiwon Lafiya ga Kowa, yana mai cewa samun magunguna masu inganci da aminci na da matukar muhimmanci ga samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya.

Hukumar ta bukaci ‘yan Najeriya su rika sayen magunguna ne kawai daga wuraren da PCN ta amince da su kuma masu nuna ingantattun lasisin aiki, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da irin wadannan ayyukan sa ido domin kare lafiyar al’umma da inganta sahihancin harkokin magunguna a kasar.