Hukumar Kula da Cututtuka da Rigakafi ta Kasa (NCDC) ta bayyana cewa annobar cutar kwalara ta harbi mutane 5,260 tare da kashe mutum 67 a jihohi 33 da Babban Birnin Tarayya (FCT), inda yara ‘yan kasa da shekara biyar suka fi kamuwa da cutar.
Sabbin alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa yawan masu kamuwa da cutar ya karu da kashi 73 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar 2025, yayin da yawan mace-macen ya ragu da kashi 37 cikin 100 sakamakon ingantaccen kula da marasa lafiya. A halin yanzu, adadin mace-mace daga cikin masu kamuwa da cutar ya kai kashi 1.3 cikin 100.
A makon kididdigar cututtuka na 22, Najeriya ta samu karin mutane 1,264 da ake zargin sun kamu da kwalara tare da mutuwar mutum 13, lamarin da ke nuna karin kashi 11 cikin 100 na masu kamuwa da cutar idan aka kwatanta da makon da ya gabata.
Rahoton ya nuna cewa maza da mata na kamuwa da cutar kusan daidai, inda maza suka kai kashi 51 cikin 100, yayin da mata suka kai kashi 49 cikin 100.
Jihar Borno ce ta fi fama da annobar, inda aka samu mutum 4,510 da suka kamu da cutar, wanda ya kai kashi 86 cikin 100 na dukkan masu dauke da cutar a Najeriya. A cikin jihar, birnin Maiduguri kadai ya yi rajistar mutum 2,706 da suka kamu da kwalara, fiye da rabin jimillar wadanda suka kamu da cutar a kasar.
Binciken muhalli da aka gudanar a Borno ya gano gurbatattun madatsun ruwa, rijiyoyin burtsatse, tankunan ruwa, magudanan ruwa da suka toshe, bututun ruwa da suka lalace, da kuma yawaitar yin bayan gida a wuraren da ba su dace ba.
Hukumar NCDC ta ce an gano cewa babu sinadarin chlorine a dukkan hanyoyin samar da ruwan da aka gwada, lamarin da ke kara haddasa yaduwar cutar.
“Hanyar yaduwar cutar na nuna ci gaba da karuwar kamuwa da ita daga mako zuwa mako, wanda ke nuna ci gaba da gurbacewar muhalli,” in ji hukumar.
Domin dakile annobar, an tanadi magungunan shan ruwa masu maye gurbin ruwa da gishiri (ORS), ruwan jinya ta jijiya (IV fluids), da kayan gwajin gaggawa. Haka kuma an horas da ma’aikatan lafiya tare da kafa cibiyoyin kula da masu cutar kwalara da wuraren bayar da ORS.
A halin yanzu, cibiyoyi uku masu dauke da gadaje 290 suna aiki tare da tallafin kungiyoyin agaji da suka hada da MSF Belgium, Save the Children da FHI360.
Hukumomi sun kuma fara aikin sanya sinadarin chlorine a ruwa, gyaran wuraren tsaftar muhalli, wayar da kan jama’a kan tsafta, da kuma kamfen din allurar rigakafin kwalara. Haka kuma ana hada kai da shugabannin gargajiya, ciki har da Shehun Borno, wajen wayar da kan al’umma domin rage yaduwar cutar.
