Gwamnatin Tarayya tare da haɗin gwiwar abokan hulɗarta na ci gaba da hanzarta aiwatar da Shirin Musamman na Yankunan Sarrafa Kayayyakin Noma na Masana’antu (SAPZ), wanda ake sa ran zai samar da sama da ayyuka 500,000 a kowace jiha tare da rage asarar amfanin gona bayan girbi a faɗin ƙasar nan.
A yayin wani taron bitar rabin wa’adin aiwatar da shirin da aka gudanar a Abuja, masu ruwa da tsaki sun tantance irin ci gaban da aka samu a mataki na farko tare da tattauna hanyoyin magance jinkirin samar da kuɗi, saye da kuma gina muhimman ababen more rayuwa.
Babban Sakataren Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci ta Tarayya, Dakta Marcus Ogunbiyi, ya bayyana SAPZ a matsayin ginshiƙi mai muhimmanci na dabarun gwamnatin na sauya fasalin harkar noma a Najeriya.
Ya ce, “An tsara shirin ne domin samar da cibiyoyin noma da masana’antu masu haɗin gwiwa waɗanda za su haɗa manoma da masana’antun sarrafa amfanin gona, wuraren ajiya, hanyoyin sufuri da kasuwanni.”
Ogunbiyi ya bayyana cewa ana aiwatar da mataki na farko na shirin a jihohi bakwai da kuma Babban Birnin Tarayya (FCT), yayin da aka tsara mataki na biyu zuwa kaso uku domin faɗaɗa shirin zuwa ƙarin jihohi.
Ya ƙara da cewa shirin na iya samar da ayyukan wucin gadi har miliyan 2.5 ta hanyar ayyukan gina ababen more rayuwa, tare da ƙara yawan amfanin gona da kashi 100 cikin ɗari, sannan ya rage asarar amfanin gona bayan girbi daga kashi 45 zuwa kashi 20 cikin ɗari.
Mai Kula da Shirin na Ƙasa, Dakta Kabir Yusuf, ya bayyana cewa an tsara SAPZ ne tare da haɗin gwiwar Bankin Raya Afirka (AfDB), Asusun Raya Aikin Noma na Duniya (IFAD), Bankin Raya Musulunci (IsDB) da gwamnatocin jihohi.
A cewarsa, manufar shirin ita ce ƙarfafa wadatar abinci, rage dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje, da kuma jawo hannun jarin kamfanoni masu zaman kansu.
Abokan hulɗar ci gaban sun bayyana sakamakon da aka samu zuwa yanzu, inda IFAD ta tallafa wa manoma 17,000 a jihohin Kano da Ogun, ta samar da ayyukan bayanan yanayi ga mutane 14,000, sannan ta raba ingantattun kayan aikin noma da iri ga manoma 9,000.
Har ila yau, IFAD ta amince da ƙarin jarin dala miliyan 50, wanda ya kai jimillar gudummawarta zuwa dala miliyan 100.
Manajan Ayyuka na AfDB, Dakta Benard Onzima, ya ce shirin yana tattara masana’antun sarrafa kayayyakin noma a yankunan da ke da ƙwarin samar da amfanin gona domin inganta samarwa da rarraba kayayyaki cikin sauƙi.
Ya bayyana cewa zuwa watan Maris na shekarar 2026, shirin ya samu alƙawarin kashe dala miliyan 86, wanda ya kai kashi 41 cikin ɗari na kasafin kuɗin da aka tsara, amma an fitar da dala miliyan 25 kacal, wato kashi 12 cikin ɗari.
Ya ce ana sa ran kafin ƙarshen shekara a kai matakin kashi 70 cikin ɗari na alƙawarin kashe kuɗi da kuma kashi 35 cikin ɗari na fitar da kuɗaɗen.
Masu ruwa da tsaki sun amince cewa SAPZ na daga cikin manyan shirye-shiryen da za su kawo sauyi a harkar noma, ta hanyar ƙara kuɗaɗen shiga na al’ummomin karkara, ƙarfafa sarkar darajar kayayyakin noma, da kuma mayar da noma wata masana’anta mai gasa a kasuwannin duniya da ke samar da kayayyakin fitarwa ƙarƙashin Ajandar Renewed Hope ta gwamnatin tarayya.
