Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta bayyana cewa kuɗaɗen da Najeriya ta kashe wajen shigo da fetur daga ƙasashen waje sun ragu da fiye da kashi 96 cikin ɗari a rubu’in farko na shekarar 2026, inda suka sauka zuwa Naira biliyan 87.4 kacal.
Rahoton ya nuna cewa wannan shi ne mafi ƙarancin adadin da aka kashe wajen shigo da fetur cikin aƙalla shekaru huɗu da suka gabata, lamarin da ke nuna tasirin ƙaruwar tace man fetur a cikin gida.
Adadin ya yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 2.27 da aka kashe a rubu’in farko na shekarar 2025. Wannan na nufin cewa daga cikin kowace Naira 100 da aka kashe kan shigo da fetur a bara, kusan Naira 4 ne kawai aka kashe a bana.
Haka kuma, fetur bai ma shiga cikin jerin manyan kayayyaki 19 da Najeriya ta fi yin ciniki da su ba a rubu’in farko na 2026.
Maimakon haka, manyan kayayyakin da aka fi shigowa da su sun haɗa da ɗanyen mai, man dizel, alkama, kayan sadarwa, motocin da aka yi amfani da su da kuma injinan noma.
Gaba ɗaya, shigo da kayayyaki ya ragu zuwa Naira tiriliyan 13.62, wanda ya nuna raguwar kashi 18.2 cikin ɗari idan aka kwatanta da bara, da kuma kashi 21.1 cikin ɗari idan aka kwatanta da rubu’in da ya gabata.
A cewar NBS, ma’aunin cinikayyar kayayyakin Najeriya ya ci gaba da nuna riba a rubu’in farko na shekarar 2026, sakamakon raguwar shigo da kayayyakin man fetur da kuma ƙarin fitar da ɗanyen mai zuwa ƙasashen waje.
Rahoton ya nuna cewa raguwar shigo da fetur ta zo ne daidai lokacin da aikin tace mai na cikin gida ke ƙaruwa, musamman daga Dangote Petroleum Refinery, wadda ta fara samar da fetur ga kasuwar Najeriya a shekarar 2024.
Hukumar NMDPRA ta bayyana cewa zuwa farkon shekarar 2026, matatar Dangote na samar da sama da kashi 90 cikin ɗari na buƙatar fetur ta ƙasa baki ɗaya.
A watan Janairu, matatar ta samar da lita miliyan 40.1 na fetur a kullum, wanda ya kai kashi 61.8 cikin ɗari na jimillar wadatar fetur. Zuwa watan Fabrairu kuwa, shigo da fetur ya ragu zuwa lita miliyan 3.1 kacal a rana, yayin da matatar Dangote ta samar da kashi 92 cikin ɗari na dukkan fetur da ake amfani da shi a ƙasar.
A watannin Maris da Afrilu, matatar ta ci gaba da mamaye kasuwa, inda take samar da tsakanin lita miliyan 34 zuwa 41 a kullum, yayin da gudunmawar fetur da ake shigowa da shi daga waje ta kasance ƙasa da kashi 10 cikin ɗari.
Masana tattalin arziki sun bayyana cewa wannan sauyi babban ci gaba ne ga ɓangaren man fetur na Najeriya, domin yana rage dogaro da ƙasashen waje wajen samar da fetur tare da rage matsin lamba kan ajiyar kuɗaɗen musayar ƙasashen waje.
Sun kuma yi hasashen cewa wannan ci gaban zai taimaka wajen ƙara daidaiton cinikayyar Najeriya da ƙasashen waje tare da ƙarfafa darajar Naira idan har samar da fetur a cikin gida ya ci gaba da biyan buƙatun ƙasar.
Tsawon shekaru da dama, Najeriya ta kasance mai dogaro sosai da shigo da fetur sakamakon rashin ingancin matatun man gwamnati. Sai dai ƙaddamar da matatar Dangote mai ƙarfin tace ganga 650,000 na mai a rana da ke Lekki ya sauya tsarin samar da fetur a ƙasar, tare da kusantar da Najeriya ga cimma cikakken wadatar makamashi daga cikin gida.
