Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya zargi Gwamnatin Tarayya da bayar da kariya da kuma tallafawa ’yan bindiga da ke addabar sassan kasar nan.
El-Rufai ya yi ikirarin cewa gwamnati na biyan ’yan bindiga kuɗin alawus na wata-wata tare da aika musu da abinci a matsayin abin da aka kira dabarar “non-kinetic,” wanda ya bayyana a matsayin manufofin “sosa zuciyar ’yan bindiga.”
“A matsayin gwamna, abinda ba zan taɓa yi ba shi ne biyan ’yan bindiga alawus na wata-wata ko aika musu da abinci a matsayin dabarar sulhu. Wannan ba komai ba ne face karfafa musu gwiwa,” in ji shi a shirin Sunday Politics na Channels Television.
Tsohon ministan birnin tarayya ya ce wannan hanya ta sassauta wa ’yan bindiga ne ke haddasa ci gaba da tabarbarewar tsaro a ƙasar.
Ya kara da cewa: “Matsayina shi ne, babu wani ’dan bindigar da ya tuba face wanda ya mutu. Mu kashe su gaba ɗaya, mu yi musu ruwan bama-bamai har sai sun zama tarihi. Sai kashi biyar cikin ɗari na su da suka rage ake iya tunanin gyarawa.”
El-Rufai ya soki manufar da ya bayyana tana ba da dama ga ’yan bindiga maimakon a hukunta su bisa laifukan da suka aikata.
“Ba za ka taɓa shawo kan abokin gaba daga raunin kai ba. Ba za ka ba shi kuɗi don ya sayi makaman zamani ya sake dawo da kai hari ba. Wannan shi ne dalilin da ya sa matsalar tsaro ta ci gaba da wanzuwa,” in ji shi.
Ya ce, “Za su iya yin shirme, su rufe gaskiya da karya, su yi propaganda, amma mutanen da ke zaune a Katsina, Zamfara, Kaduna da sauran jihohin da abin ya shafa sun san gaskiyar abin da ke faruwa. Ku bari lokacin ya yi, za mu bayyana dukkanin gaskiya.”
A halin yanzu, Gwamnatin Tarayya ba ta mayar da martani kan wannan zargi na El-Rufai ba.
Sai dai a baya, Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa (NSA), Nuhu Ribadu, ya bayyana a watan Yuli cewa hare-haren Boko Haram, ayyukan ’yan bindiga da rikice-rikicen al’umma a Arewa sun ragu sosai a cikin shekaru biyu na mulkin Shugaba Bola Tinubu, idan aka kwatanta da gwamnatin da ta gabata.
Ribadu ya ce a lokacin gwamnatin da ta gabata, mutum 1,192 aka kashe a Jihar Kaduna tare da sace fiye da 3,348, yayin da a Jihar Benue aka kashe mutane sama da 5,000.
Ya bayyana hakan ne yayin wani taron shugabannin Arewa da Cibiyar tunawa da Sir Ahmadu Bello ta shirya a Kaduna.
NSA ɗin ya ce nasarorin da aka samu wajen yaki da rashin tsaro sun samo asali ne daga umarnin Shugaba Tinubu na samar da hadin kai tsakanin hukumomin tsaro.
Ya ce a halin yanzu, hare-haren sojoji a Arewa maso Yamma sun taimaka wajen kubutar da mutum 11,259 da aka yi garkuwa da su, tare da hallaka shugabannin ’yan bindiga da dama a Zamfara, Kaduna da Katsina.
Haka kuma, a watan Afrilu Ribadu ya shawarci ’yan Najeriya da su daina biyan kuɗin fansa ga ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

