Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga ta Najeriya (NRS) ta ƙaddamar da wani sabon tsarin gudanar da haraji na zamani mai suna Rev360, wanda aka tsara domin gano masu kauce wa biyan haraji tare da sauƙaƙa wa masu biyan haraji bin dokokin haraji.
Shugaban Hukumar, Dakta Zacch Adedeji, ya bayyana Rev360 a matsayin wani babban ci gaba da zai taimaka wajen sauya tsarin gudanar da haraji zuwa matakin Tax Administration 3.0, ta hanyar inganta ayyukan hidima, kula da bin dokokin haraji, tabbatar da gaskiya da kuma ƙarfafa hulɗa da masu biyan haraji.
Ya ce, “Ƙaddamar da wannan tsari na nuna ƙudirinmu na ci gaba da amfani da sabbin fasahohi, sauya tsarin aiki zuwa na zamani, da kuma gina tsarin tattara kuɗaɗen shiga mai inganci, gaskiya da kuma saurin amsa bukatun jama’a.”
Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Harkokin Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, wanda Mohammed Sanusi ya wakilta a wajen taron, ya yaba da wannan mataki, yana mai cewa tsarin haraji da ke amfani da fasahar zamani yana da muhimmanci wajen samar da yanayin kasuwanci mai sauƙi da tabbas wanda ke tallafa wa ci gaban tattalin arziki da ƙasa baki ɗaya.
Ya tabbatar da cewa ma’aikatar za ta ba da cikakken goyon baya wajen aiwatar da Rev360, yana mai bayyana shi a matsayin mataki na farko na wani babban shiri na sauya tsarin haraji domin sauƙaƙa hulɗar masu biyan haraji da gwamnati tare da ƙara amincewa da tsarin.
An tsara Rev360 domin inganta rajistar masu biyan haraji, gabatar da bayanan haraji, sarrafa biyan kuɗaɗe, bibiyar bin dokokin haraji da kuma samar da ayyukan tallafi, tare da ba masu amfani da shi damar samun sauƙi da cikakken bayani a kowane lokaci.
Darakta Mai Kula da Fasaha na Hukumar, Iniabasi Akpkan, ya bayyana cewa sabon tsarin zai sa biyan haraji ya zama cikin sauri da sauƙi, lamarin da zai ƙarfafa mutane da kamfanoni su biya harajinsu da son rai.
A cewarsa, “Idan mutane za su iya biyan haraji cikin sauƙi, za su biya cikin gaggawa kuma daga ofisoshinsu ko gidajensu ba tare da wata wahala ba.”
Ana sa ran wannan shiri zai ƙara amincewar masu zuba jari, ya inganta matsayin Najeriya a fannin sauƙaƙe gudanar da kasuwanci, tare da tallafa wa manufofin gwamnatin tarayya na gyaran tattalin arziki.
Masana sun bayyana cewa Rev360 zai kafa tubalin wani tsarin gudanar da haraji na zamani da ke amfani da bayanai da fasahar basira, wanda zai taimaka wajen inganta tattara kuɗaɗen shiga da kuma rage kauce wa biyan haraji a Najeriya.
