Trends

Neman Filayen Mai: Gwamnatin Tarayya ta Ƙayyade 12 ga Yuni a Matsayin Ranar Ƙarshen

Gwamnatin Tarayya ta Najeriya, ta hannun Hukumar Kula da Masana’antar Man Fetur ta Ƙasa (NUPRC), ta sanya ranar Juma’a, 12 ga Yuni, 2026, a matsayin ƙarshe na karɓar takardun neman filayen mai (technical da commercial bids) a zagayen lasisin 2025 da ake ci gaba da gudanarwa.

A sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce: “Karɓar takardun fasaha da na kasuwanci daga masu neman lasisi da aka riga aka tantance a zagayen 2025 zai rufe a ranar Juma’a, 12 ga Yuni, 2026, da ƙarfe 4:30 na yamma (WAT), bisa ga ƙa’idojin zagayen lasisi na 2025.”

Wannan mataki na nuna wani muhimmin lokaci a aikin bayar da lasisin, yayin da masu zuba jari ke fafatawa domin samun filayen mai a Najeriya, a daidai lokacin da gwamnati ke ƙoƙarin jawo jari da ƙara yawan samar da danyen mai.

Zagayen lasisin 2025, wanda aka ƙaddamar a watan Disamba, ya ƙunshi filayen mai da iskar gas guda 50, ciki har da 15 na ƙasa (onshore), 19 na ruwa mai zurfi kaɗan (shallow water), 15 na yankunan bincike na gaba (frontier), da kuma ɗaya na ruwa mai zurfi sosai (deep water). Ana sa ran zai jawo jarin kusan dala biliyan 10.

Hukumar NUPRC ta yi hasashen cewa wannan zagaye zai iya buɗe damar hakar ganga biliyan 2 na mai cikin shekaru goma masu zuwa, tare da ƙara yawan samar da mai da kusan ganga 400,000 a kowace rana idan aka ci gaba da aiwatar da shi yadda ya kamata.

An riga an kammala matakin tantancewa a watan Maris, inda aka sanar da waɗanda suka yi nasara. Hukumar ta kuma ce tana shirin fara zagayen lasisi na 2026, wanda ya riga ya samu amincewar ma’aikatar mai, kuma zai fara a kashi na uku (Q3) na 2026.

Shugabar NUPRC, Oritsemeyiwa Eyesan, ta bayyana cewa hukumar na ƙoƙarin tabbatar da cewa ana gudanar da zagayen bayar da lasisin mai a duk shekara ƙarƙashin dokar Petroleum Industry Act, domin tabbatar da gaskiya, buɗaɗɗen gasa, da kuma ingancin rabon filayen mai.

Rahoton ya ce kammala matakin karɓar bids ɗin zai buɗe hanya ga bayar da lasisin filayen mai, wanda zai ƙara ƙarfafa dabarun Najeriya na faɗaɗa binciken mai, ƙara yawan arziki, da kuma tabbatar da ci gaba da jawo hankalin masu zuba jari a ɓangaren makamashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *